Kasuwancin tabarma ta yi mini komai a rayuwa – Abdussalam Ibrahim
Abdussalam Ibrahim wani matashi ne mai sana’ar sayar da tabarmi da adudu da kuma sauran kayayyakin gargajiya a Kalaba Jihar Kuros Riba. Ya shafe shekara sama da talatin yana wannan sana’a. A hirarsu da wakilinmu, ya bayyana cewa babu abin da zai ce a wannan sana’a illa sai godiya ga Allah Madaukakin Sarki, domin ta […]

Abdussalam Ibrahim wani matashi ne mai sana’ar sayar da tabarmi da adudu da kuma sauran kayayyakin gargajiya a Kalaba Jihar Kuros Riba. Ya shafe shekara sama da talatin yana wannan sana’a. A hirarsu da wakilinmu, ya bayyana cewa babu abin da zai ce a wannan sana’a illa sai godiya ga Allah Madaukakin Sarki, domin ta yi masa asin-da-asin. Ya mallaki gidaje da kaddarori
Aminiya: Ga shi na ga kana dauke da tabarmi da adudu da ragaya da kuma bulala, har ma da mafeci, ko yaya ake kiran wannn sana’a taku?
Abdussalam: A Hausance sunanta tallar tabarma.
Aminiya: Yau kimanin shekara nawa ke nan kana wannan sana’a?
Abdussalam: A takaice dai in bayyana maka, zan kai shekara 35 ina wannan sana’a.
Aminiya: Yadda ka ambaci yawan shekarun da ka yi kana wannan sana’a, ga alama gadon ta ka yi ke nan?
Abdussalam: Gaskiya wannna sana’a tamu gadonta muka yi kuma harkar nan alhamdu lillahi.
Aminiya: A da can duk wani mutumin Arewa ya san akwai adudu, ragaya da sauransu, sai ga shi yanzu an samu sauyin zamani; maimakon tabarmar kaba sai ta roba, kabar ce babu ko kuwa karanci ta yi aka koma roba?
Abdussalam: Alhamdu lillahi, wannan tambaya da ka yi min na ji dadi. Sakamakon wannan tabarma da kake fada ta kaba akwai ta ba babu ba amma yanayin zamani da muke fuskanta, mutane sun yi sauki da sayen wannan tabarmar kaba sai wadda suka zaba kuma yanzu ta zamanin ita suka fi zaba, ita aka fi saye a yanzu. Haka muna nan muna dauke da wannan ma ta da ga duk mai bukata.
Aminiya: Dayake nan kurmi ne, kun taba kawo tabarmar kaba, ’yan yankin nan suna saye?
Abdussalam: kwarai ma kuwa hakika, ko yanzu ma akwai ta.
Aminiya: Ya za ka kwatanta cinikin tabarmar kaba da ta zamani?
Abdussalam: Alhamdu lillahi. E, to gaskiya ita ta kabar da wannan ta zamani idan ka sayo ta kabar guda 50, ka sayo ta zamani guda 30; za ka yi saurin sayar da ta zamanin saboda ta fi tsada fiye da ta kaba.
Aminiya: Wato hakan ya kawo sauyi a sana’ar taku ke nan?
Abdussalam: E, matuka.
Aminiya: Da a Arewa ana sayen tabarmi ne ana shimfidawa a wuraren da jama’a ke hutawa, masallatai da sauransu, a naka tunani me kake ji ’yan asalin wannan yanki ke yi da tabarmar idan sun saya?
Abdussalam: Alhamdu lillahi, wannan tambaya da ka yi na ji dadin ta don na san kadan daga ciki.
Aminiya: To, ai sai ka gaya mana?
Abdussalam: Babban yakini a nan da zan gaya maka, suna sayen ta a kan kwanciyar zafi idan lokaci ya yi, wadansu kuma idan nasu ya mutu suna tafiya da ita makabarta su shimfida ta bayan sun gama wannan al’ada tasu.
Aminiya: Bari mu dawo kan adudu, ragaya, na ga ma har da bulala da sauran tarkace; nan ba Arewa ba ce, al’adu sun bambanta, na lura da ba su yin danki, jeren daki ko ajiya a ragayar mata, ’yan yankin nan suna sayen adudu da ragayar?
Abdussalam: Suna saye suna ajiye kaya da suturunsu.
Aminiya: Kana nufin kamar akwati suke yi da ita?
Abdussalam: Ka ji magana ke nan, ai a kan haka ne ma nake ma magana.
Aminiya: Dayake kowane allazi da nasa amanu, wadanne matsaloli kuke fuskanta a wannan sana’a?
Abdussalam: Na’am, gaskiya matsalar da muke fuskanta a wannan sana’a ita ce juyawar lokaci.
Aminiya: Da ka ce juyawar lokaci, mai karatu zai so sanin ma’ana.
Abdssalam: Yanayi na ruwan sama da ake yi kamar na yanzu idan ana marka-marka, hakika cinikin yana ja baya ba kamar lokacin da ba a ruwan sama ba.
Aminiya: Kasancewar kasar nan ta shiga wani yanayi na lalacewar tsaro, ana kiran ’yan Arewa da sunan Boko Haram, ko kai ma ka taba fuskantar wannan matsala?
Abdussalam: E, gaskiya abin yana bata mana rai, maganar da nake yi da kai yau din nan, akwai wani bawan Allah da naje wata kasuwa da ke bakin ruwa yawon talla; na zo wucewa shi ma zai wuce sai tabarmata ta dan taba shi, ya ce da ni Boko Haram. Ni kuma da yake ina dan jin Turanci sai na bude masa wuta ina zazzagarsa. Nan take ’yan uwansa suka taso suna ba ni hakuri, suna cewa in yi hakuri mashayi ne, a buge yake.
Aminiya: Tsawon shekara talatin da biyar kana wannan sana’a, ko kwalliya ta biya kudin sabulu?
Abdussalam: Alhamdu lillah,i ai na yi gida, na yi mata biyu, na yi mota, na sayi babur. Ai ni alhamdu lillahi kuma yanzu ina tsakiyar harkar nan.
Aminiya: Mene ne babban burinka a wannan sana’a, kara aure ko kuwa?
Abdussalam: Ni yanzu abu daya kawai nake fuskanta.
Aminiya: Me ke nan?
Abdussalam: Mota kawai da nake jigila da ita, idan na koma gida me ya rage mini? Ga mata ga gonaki na saya, ga mota ai alhamdu lillahi.