Kasuwar Dawanau: Jagorar kasuwannin hatsi a Najeriya

Kasuwar Danawau ta duniya da ke Jihar Kano kasuwa ce da ke kasuwancin hatsi na tsawon lokaci. Asali an kafa kasuwar ce domin ta zama wajen kasuwanci da adana hatsi da sauran albarkatun gona a jihar. Amma kasuwar ta bunkasa zuwa inda take samar da kayan abinci ba wai a Najeriya ba kawai har zuwa […]

Kasuwar Dawanau: Jagorar kasuwannin hatsi a Najeriya

Kasuwar Dawanau: Jagorar kasuwannin hatsi a Najeriya

Kasuwar Danawau ta duniya da ke Jihar Kano kasuwa ce da ke kasuwancin hatsi na tsawon lokaci. Asali an kafa kasuwar ce domin ta zama wajen kasuwanci da adana hatsi da sauran albarkatun gona a jihar.

Amma kasuwar ta bunkasa zuwa inda take samar da kayan abinci ba wai a Najeriya ba kawai har zuwa kasashen Arewa maso Yammacin Afirka.

Wani mai hada-hada a kasuwar ta Dawananu Alhaji Habibu Auwal Gezawa ya bayyana cewa, an assasa kasuwar ce domin samar da hatsi irinsu dawa da masara kafin daga bisani ta rikide zuwa wata babbar cibiyar samar da nau’ukan kayan abinci.

Aminiya ta gano cewa kusan babu nau’in kayan abinci da ba a sayarwa a kasuwar kamar su gero, da dawa, da masara, da wake, da waken suya, da alkama, da shinkafa, sai kuma zobo, da jinja da dai sauransu.

Wani abin sha’awa game da kasuwar shi ne yadda ’yan kasuwa daga lungu da sakon Najeriya da kuma kasashen Yammacin Afirka ke shigowa a kullum. Bayanai na nuna cewa mafi yawan waken da ake sayar wa a kasuwar yana fitowa ne daga Jamhuriyar Nijar.

A baya-bayan nan ’yan kasuwa daga kasashen India da China ma sun bi sahu, inda suke sayan kaya daga kasuwar kuma su yi safararsa zuwa kasashensu.

Mukaddashin Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar, Alhaji Mur¬tala Muhammad wanda aka fi sani da Murtala Danmutum ya ce kasuwar ta kafu ne sama da shekara 46 da suka shude kuma tana da dadadden tarihin alakar kasuwanci da mutanen Nijar, da Chadi, da Kamaru da wasu kasashen yammacin Afirka.

Ya ce, “Asali kasuwar ta kasance wata cibiya ta tattara kayan abinci musamman dawa da kuma gero saboda amfanin cikin gida.

“Amma saboda dakatar da safarar kayan abinci da gwamnati ta yi, kasuwar a kwanan nan sai ta rikida zuwa cibiyar safarar kayan gwari. Kasashen Yammacin Afirka suke sayan kashi 45% na kayayyakinmu a kullum,” inji Murtala Danmutum.

Ya kara da cewa yanzu haka an fadada kasuwancin wadannan kayayyakin zuwa Amurka, da Asiya da Turai, inda ya ce akalla tirelan 50 zuwa 70 na hatsi ke fita daga kasuwar a kullum domin kai wa kasuwannin cikin gida Najeriya, sannan kuma kusan tirela 100 zuwa 150 suke fita zuwa kasashen Afirka a kullum.

Ya ce yawancin kayyakin a nan gida Najeriya ake noma su, sai kuma makwabciyarmu Nijar, “duk da cewa kasuwar tsohuwa ce ba ta kayan zamani, safarar kayayyakin daga kasuwar na kara samun armashi. Akwai akalla manyan kamfanonin duniya guda 200 da suke harkokin kasuwanci a kasuwar. Harkokin kasuwancin na kara habaka a kasuwar fiye dad a. Akwai akalla mutum 4000 da suke cin abinci a kasuwar, sannan kuma ga batun samar da kudin shiga ga gwamnati,” inji shi.

Shugaban ya kara da cewa domin tabbatar da an ci gaba da samun nasara da cigaba da ake samu a kasuwar, akwai bukatar gwamnatin jiha ta zamanantar da kauswar da kuma gina Katanga domin samar da tsaro, da kuma samar da hanya domin saukake wa ’yan kasuwa.

Malam Hamisu Dan Wawa mai sana’ar hatsi wanda ya kasance yana kasuwanci a Kasuwar Danawau fiye da shekara 34 da suka wuce ya ce kasuwar ta samar mutane masu miliyoyin kudi da yawa.

Dan Wawu ya kara da cewa da can kasuwar ta ’yan Najeriya ce kawai, inda ya nuna takaicinsa da yadda, “’Yan Indiya da China suka cika kasuwar suke neman mamaye ta. Mutane ba za su gane ba, a da can kasuwar ’yan Najeriya ne ke rike da kasuwar, amma yanzu kasuwar ta fara komawa wajen ’yan kasashen waje, kuma mutanenmu ne suke musu aiki.

“Idan za a yi kididdigar gano kamfanonin da suke kasuwar a yanzu, za a gano cewa an kwace kasuwancin da ke wakana a Kasuwar Dawanau daga ’yan kasuwannin cikin gida.”

Shi ma a nasa jawabin, wani tsohon manomi a Jihar Kano Alhaji Umaru Ado, cewa ya yi ya kamata a samar da doka da za ta lura da yadda ake fitar da abinci daga Kasuwar Danawau domin idan ba a yi hakan ba, za a iya samun matsalar rashin abinci a Najeriya.

Ado ya kara da cewa duk da cewa akwai alamar cewa bana yabanya ta yi kyau, hanya daya da gwamnati za ta magance matsalar fitar da hatsi daga kasuwar ita ce samar da hukomomi a duk jihohi domin su rika lura da kasuwanci da kasuwanni a kasuwar da ma kasuwannin kasar baki daya.

“Yana da kyau a samar da hukomomin lura da kasuwanni a kasar. A matsayina na dan kasuwar hatsi kuma manomi, ina bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnati ta samar da hukomomin kula da kasuwanci a kasar nan baki daya.”