Kasuwar hannayen jari ta samu karin Naira biliyan 48
Hada-hadar hannayen jarin da aka gudanar a kasuwar hannun jari ta Najeriya a makon jiya ta samu karin Naira biliyan 48. Binciken Aminiya ya gano cewa kasuwar ta samu karin ne saboda ribar da wasu kamfanoni suka samu, inda jarin kasuwar ya karu daga Naira tiliriyan 9.20 zuwa Naira tiriliyan 9.25.Kamfanin Seplet shi ne ya […]
Hada-hadar hannayen jarin da aka gudanar a kasuwar hannun jari ta Najeriya a makon jiya ta samu karin Naira biliyan 48.
Binciken Aminiya ya gano cewa kasuwar ta samu karin ne saboda ribar da wasu kamfanoni suka samu, inda jarin kasuwar ya karu daga Naira tiliriyan 9.20 zuwa Naira tiriliyan 9.25.
Kamfanin Seplet shi ne ya fi samun riba, inda hannun jarinsa ya tashi daga Naira 19 zuwa Naira 404 ga hannun jari daya. Kamfanin mai na Forte Oil shi ma ya ci riba, inda hannun jarinsa ya tashi daga Naira 7.91 zuwa Naira 220. Kamfanin Nestle shi ma hannun jarinsa ya tashi daga Naira 7.25 zuwa Naira 753.50 a duk hannun jari daya. Kamfanin dangote shi ma ya samu karuwa daga Naira 2.09 zuwa Naira 143.99.
Haka ma kamfanin lemon kwalba na 7UP da hannun jarinsa ya kai kwabo 85 ya tashi zuwa Naira 150 a kowane hannun jari. Kamfanin CAP shi ya fi kowane kamfanin faduwar hannun jari, inda hannun jarinsa ya ragu da Naira 1.93 ga kowane hannun jari. Kamfanin Beta Glass da kamfanin Fulawa sun samu ragi da Naira 1 da kwabo 50 zuwa Naira 1 da kwabo 33 a kowane hannun jari.