Kasuwar hannun jari ta farfado

Ga alama kasuwar hannayen jari ta farfado daga asarar da ta yi ta Naira biliyan 800 sakamakon dage zabe da hukumar zabe ta yi a cikin watan jiya, inda a yanzu kasuwar ta samu ribar Naira biliyan 198. Aminiya ta gano cewa hannayen jarin kamfanoni sun samu karin tagomashi daga jama’a, inda aka yi hada-hadar […]

Kasuwar hannun jari ta farfado

Ga alama kasuwar hannayen jari ta farfado daga asarar da ta yi ta Naira biliyan 800 sakamakon dage zabe da hukumar zabe ta yi a cikin watan jiya, inda a yanzu kasuwar ta samu ribar Naira biliyan 198.

Aminiya ta gano cewa hannayen jarin kamfanoni sun samu karin tagomashi daga jama’a, inda aka yi hada-hadar da aka samu karin kashi 2.01 inda kuma aka samu fiye da Naira tiriliyan 10 bayan an rufe kasuwar.
Tagomashin da kasuwar ta samu sakamakon hada-hadar hannayen jarin da aka yi a kasuwar hannayen jari da ke Jihar Legas sun karu da kashi 541.74, wanda hakan yake nuna samun kashi 1.83.
Hakan ya nuna an yi hada-hadar hannun jari sau 84, 641, wato kimanin Naira biliyan 7 da dubu 735 kwatankwacin Naira biliyan 92 da dubu 245 a karshen watan jiya.
Kamfanin da ke sarrafa kayayyakin amfanin yau da kullum su ne suka fi samun riba, sannan kamfanin da suke sarrafa abubuwa iri-iri suka biyo bayansu.
Kamfanin man fetur na Saplat Petroleum Debelopment Company shi ne ya fi kowane kamfani samun riba, inda ka sayi hanun jarinsa daga Naira 164.77 zuwa 470 a kowane hannun jari daya.
Kamfanin mai na Forte Oil shi ya jagoranci kamfanoni 10 da hannayen jarinsu ya fadi, wadanda suka hada da kamfanin giya na Guinness da kamfanin mai na Total da kamfanin mai na Conoil da kamfanin giya na Breweries da kamfanin siminti na dangote da kamfanin Gilashi na Beta Glass Company.
Sauran sun hada da kamfanin Filawa na Flour Mill Nigerian Plc da kamfanin Cadbury da kuma kamfanin siminti na Ashaka.