Kasuwar hannun jari ta samu tagomashi
Kasuwar hada-hadar hannun jari ta Najeriya ta ci gaba da samun tagomashi inda ta samu karin Naira biliyan 335 ta rufe da Naira tiriliyan 15 da 782. Daukacin hannayen jarin da aka yi hada-hadarsu sun karu da kasha biyu da digo 17 a cikin dari inda ta rufe da fiye da kashi 44 cikin […]
Kasuwar hada-hadar hannun jari ta Najeriya ta ci gaba da samun tagomashi inda ta samu karin Naira biliyan 335 ta rufe da Naira tiriliyan 15 da 782.
Daukacin hannayen jarin da aka yi hada-hadarsu sun karu da kasha biyu da digo 17 a cikin dari inda ta rufe da fiye da kashi 44 cikin dari.
Hakan ya nuna hada-hadar hannayen jarin da aka gudanar a kasuwar sun karu idan aka kwatanta da hada-hadar hannayen jarin shekarun baya.