‘Kasuwar hatsi ta Saminaka tana taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya’
Kasuwar hatsi ta garin Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi suna wajen gudanar da harkokin saye da sayar da kayayyakin amfanin gona musamman masara a Najeriya da sauran kasashen makwabta. Ita dai wannan kasuwa wadda aka bude a garin Saminaka tun a shekarar 1968 tana ci a duk ranar Laraba a kowanne mako.A cewar […]
Kasuwar hatsi ta garin Saminaka da ke Jihar Kaduna ta yi suna wajen gudanar da harkokin saye da sayar da kayayyakin amfanin gona musamman masara a Najeriya da sauran kasashen makwabta. Ita dai wannan kasuwa wadda aka bude a garin Saminaka tun a shekarar 1968 tana ci a duk ranar Laraba a kowanne mako.
A cewar Sarkin kasuwar Malam Isah Manu Idris an kafa wannan kasuwa ne don a habaka harkokin saye da sayar da kayayyakin amfanin gona. Kuma a cikin ikon Allah wannan kasuwa ta yi suna daga ko’ina a Najeriya har da kasashen da suke makwabtaka da Najeriya.
Ya ce babu shakka wannan kasuwa tana taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Domin a kowanne mako kamfanoni daban daban daga ko’ina a Najeriya da kasashen makwabta suna sayen kayayyakin amfanin gona a wannan kasuwa, musamman daga kudancin Najeriya.
Ya ce “Muna samun kayayyakin amfanin gonar ne a wannan kasuwa daga kauyukan da ke wannan yankin na Saminaka da sauran yankunan jihohin Bauchi da Kano da Filato da ke makwabtaka da wannan yanki.”
“Wannan kasuwa tana taimakawa wajen bunkasa harkokin noma a wannan yanki, domin idan manoman wannan yanki suka noma kayayyakin amfanin gona sukan kawo wannan kasuwa su sayar.
“Muna da daruruwan lebirori da suke amfana da wannan kasuwa, kuma akwai ‘yan kasuwar da suke saya wa baki kayayyakin amfanin gona a wannan kasuwa su ma suna amfana. Sannan karamar Hukumar Lere tana samun kudin shiga a wannan kasuwa. Don haka al’ummar karamar Hukumar Lere da Jihar Kaduna da Najeriya gaba daya suna matukar amfana da wannan kasuwa ta bangarori da dama.” Inji shi.
Malam Isah ya ce amma duk da haka suna fama da matsalolin rashin gyara a wannan kasuwa, domin tana bukatar manyan shagunan da ‘yan kasuwarmu za su rika ajiya da hanyoyin mota.
Ya ce a gaskiya “Muna fuskantar cunkoso a wannan kasuwa musamman a ranar Laraba da kasuwar take ci, saboda matsalar rashin hanyoyin mota a kasuwar. Don haka ya yi kira ga karamar Hukumar Lere ta dubi wadannan matsaloli don ta magance su.”
Ya bukaci gwamnatin Jihar Kaduna da ta tarayya kan su bude kamfanin sarrafa kayayyakin amfanin gona a wannan yanki, domin yin hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma da kasuwanci a yankin.