Kasuwar jar hula da farar shadda ta habaka a Kano

A yanzu haka kasuwancin farar shadda da na jan hula na ci gaba da habaka a Jihar Kano sakamakon ziyarar da ake sa ran tsohon Gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar 30 ga watan nan, lamarin da ’yan kasuwar ke cewa su kam sai sam barka. Binciken Aminiya ya gano tun daga hawan […]

Kasuwar jar hula da farar shadda ta habaka a Kano

A yanzu haka kasuwancin farar shadda da na jan hula na ci gaba da habaka a Jihar Kano sakamakon ziyarar da ake sa ran tsohon Gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar 30 ga watan nan, lamarin da ’yan kasuwar ke cewa su kam sai sam barka.

Binciken Aminiya ya gano tun daga hawan mulkin sa a shekarar 2011 Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso  ya mayar da farar shadda da jar hula a matsayin suturarsa, wanda magoya bayansa da yawa suka fara kwaikwayonsa, lamarin da ake yi wa take da kwankwasiyya.

Sai dai a wanann karon da tsohon Gwaman yake niyyar kawo ziyara abin ya kara bunkasa domin kusan dukkanin wani mabiyinsa yana kokarin tanadar irin wannan sutura don nuna cikakken goyon baynasa ga darkar ta Kwankwasiyya.

Bnciken Aminiya ya gano cewa jar hular da mabiyan Kwankwasiyyar ke sanya wa tana da sunaye daban-daban, wadanda ake alakanta su da kungiyar kamar Mahdi  da Ganduje da  kuma kwankwasiyya “kin ga hulunan ga su nan guda uku muke da su akwai wacce ake kira Mahdi ita ce aka fi yayinta a wanann lokaci, domin a yanzu idan za ki zaga kasuwa ba za ki same ta ba, domin da zarar an kawo ta to a ranar take karewa tas. Sai kuma Ganduje ita kuma an yi mata zanen farin layi daya, wato wai ana nufin Ganduje zagayen mulkin JIhar Kano daya tak zai yi sai kuma sauran gama garin jajayen huluna wadanda ake kira da kwankwasiyya kawai. Lamarin ba akan hulunan kawai ya tsaya ba domin ya shafi wata jar atamfa, wacce ake kira buberry kasancewar teloli na sayen atamfar ana dinka hulunan kwankwasiyya da ita” kamar yadda wani mai sana’ar huluna a Kantin Kwari mai suna Alasan Usman ya bayyana.

Har ila yau Alasan ya shaida wa Aminiya cewa a yanzu a rana daya yakan sayar da huluna kimanin 30 zuwa 40 a sabanin a baya da bai iya saya da huluna 10 ba.

Shi ma Yusuf Muhammad wani mai sayar da huluna a dai Kasuwar Kantin Kwari ya bayyana cewa, a yanzu haka saboda bukatar da ake yi na jar hula ya kawo karancin hulunan a kasuwa. 

“Kin ga yanzu babu hulunan ma a kasuwa. Da zarar an kawo ba su jimawa sun kare.  Dama daga kauyuka ake kawo mana.  Ga shi kuma masu sayen kullum karuwa suke yi, domin wasu am daga wasu garuruwan suke zuwa. Sai dai watakila yanzu ina hangen za a samu saukin lamarin , kasancewar a yanzu na ga telolinmu a nan  sun fara dinka ire-iren jajayen hulunan.” 

Wani da ya zo kasuwa don mai sayen jar hula mai sunan Umar Isa ya tabbatar wa Aminiya cewa ba wai mutanen Kano ne kadai ke rige-rigen sayen jar hular ba, har ma daga wasu garuruwan da ke fadin kasar nan. 

“Kin ga ni wannan hular da na zo saye abokina ne daga Bauchi ya yi min waya na saya masa. Kin san mutane suna son Kwankwaso, suna kuma son ya tsaya takarar shugaban kasa” Inji shi.

Alhaji Sani Muhamamd mai sayar da shadda a cikin kasuwar Kantin Kwari ya shaida wa Aminiya cewa ba wai kawai kasuwar farar shada ce ta bude a wanann lokaci ba hatta farin yadi ma mutane na nemansa don dinkawa. 

“Wani lokacin ma sai dai ka yi ta bin dilolin kayan ka samu su ba ka kayan don gudun yankewarsu a kasuwa.  Shi ya sa ma mutane yanzu suke amfani da farin yadin domin babu shaddar kamar da a kasuwa.” Inji shi.

 

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno