Kasuwar kaji ta yi sababbin shugabanni
’Yan kasuwar kaji da ke garin Jos babban birnin Jihar Fi sababbin shugabanninsu a makon jiya. Shugabannin ‘yan kasuwar da aka zaba sun hada da Alhaji Sani Abdul’azez (Shugaba) da Alhaji Habibu Ahmed (Mataimakin shugaba) da Buhari Shu’aibu (Sakatare) da Sagiru Sani a matsayin Ma’aji.Sauran shugabannin su ne: Nasiru Sakataren Kudi da Abdurrahaman Muhammad Mai […]
’Yan kasuwar kaji da ke garin Jos babban birnin Jihar Fi sababbin shugabanninsu a makon jiya.
Shugabannin ‘yan kasuwar da aka zaba sun hada da Alhaji Sani Abdul’azez (Shugaba) da Alhaji Habibu Ahmed (Mataimakin shugaba) da Buhari Shu’aibu (Sakatare) da Sagiru Sani a matsayin Ma’aji.
Sauran shugabannin su ne: Nasiru Sakataren Kudi da Abdurrahaman Muhammad Mai binciken kudi da Ahmed Sani Sakataren Tsare-tsare da Ahmed Abdullahi Jami’in hulda da jama’a da kuma Alhaji Yakubu Muhammad Jami’in tsaro.
Da yake jawabi bayan kammala zaben sabon shugaban kasuwar Alhaji Sani Abdul’azez ya mika godiyarsu ga dukkan ’yan kasuwar kan zaben su da suka yi.
Ya ce “Da yardar Allah za mu yi iyakar kokarinmu wajen ganin mun kare dukkan hakkoki da mutuncin ’yan kasuwar da suke gudanar da harkokin kasuwanci a wannan kasuwa.”
Ya ce za su yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun kawo abubuwan da za su kawo ci gaba a wannan kasuwa.
A karshe ya bukaci dukkan ’yan kasuwar su hada kai, su kuma yi hakuri da juna don a samu ci gaba a kasuwar tasu.