Kasuwar Karu da ke Abuja ta yi gobara

A cikin dare gobarar ta tashi kuma ana bincike domin gano abin da ya haddasa tashinta

Kasuwar Karu da ke Abuja ta yi gobara

Yadda ake kashe wata gobara da ta tashi a wata kasuwa a Yola

Gobara ta lukume kadarorin miliyoyin kudade a Kasuwar Karu da ke yankin babban birnin tarayya, Abuja, a cikin dare.

Mukaddashin Daraktan hukumar kashe gobara ta Abuja, Abiola Adebayo, ya ce an baza jami’an kashe gobara a wurin kuma ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.

Aa safiyar Juma’a, wani mazaunin garin Karu, Yusuf Mustapha, ya shaida wa wakilinmu cewa wutar ta kona kayayyakin miliyoyin Naira kurmus.

“Gaskiya ne; an yi mummunar gobara a kasuwar Karu tun da misalin karfe 8 na daren jiya kuma ta duki wasu sa’o’i tana ci.

“Wutar ta yi barna mai girkma, abin takaici ne, ina da abokai da ke kasuwanci a kasuwa,” in ji Mustapha.

Kakakin ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh, a wata sanarwa da ta fitar, ta ce an tura ’yan sanda zuwa wurin.

“Sakakamkon tashin gobarar, kwamishinan ’yan sandan Abuja, Benneth C. Igweh, ya yi gaggawar tura ’yan sanda masu sintiri daga sassan Karu, Nyanya, da Jikwoyi tare da jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya.

­“Za su ba da gudummawa wurin don kashe gobarar, tare da dakile duk wani yunƙuri na sace abin da ke cikin shagunan kasuwar da kuma kare wasu kayayyaki masu daraja daga konewa. Za a sanar da ci gaba da ci gaba a kan lokaci,” in ji sanarwar.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana