Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara
Gobarar da ta tashi a cikin dare ta laƙume dukiyar miliyoyin Naira a Kasuwar Laranto da ke Jos, Jihar Filato.
Gobara ta laƙume dukiyar miliyoyin Naira a Kasuwar Laranto da ke Jos, Jihar Filato.
Wutar ta tashi ne da misalin ƙarfe 11 na dare bayan an tashi kasuwar, sai daga baya mutane suka kawo ɗauki.
Shugaban ƙungiyar ’yan kasuwar, Alhaji Idris Shehu, ya tabbatar wa wakilinmu cewa, “Gobarar ta laƙume ɓangaren ’yan katako da ɓangaren masu sayar da tufafin Gwanki da ɓangaren kayan daƙi.”
Ya ƙara da cewa ana ci gaba aiki, ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba.
- Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos
- Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano
- Yadda jiragen yaƙi suka halaka ’yan ta’adda a Zamfara
Shugaban ’yan katako a kasuwar, Umar Aliyu, ya ce da jami’an kashe gobara sun kawo ɗauki da wuri, da asarar da aka yi ba ta kai haka ba.
Koda yake ba a tantance girman ɓarnar ta yi ba.
Ya bayyana cewa ko “da aka a kai wa jami’an rahoto, ba su zo ba, suka ce babu mai a motocinsu.
“Haka matsa musu amma suka dage cewa babu mai a motocin.
“Sai bayan da Shugaban Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da Kwamishinan Ruwa suka zo kasuwar, suka kira jami’an kwana-kwanan da ke gidan Gwamna, sannan suka kawo ɗauki suma kashe gobarar.”
Kasuwar Laranto na yawan fama da gobara kusan kowace shekara.
Ko a shekarar da ta gabata irin haka ta faru a ɓangaren ’yan katako, sakamakon matsalar wutar lantarki.