Kasuwar Maigatari na samar da kudin shiga Naira miliyan biyu duk wata
Shugaban karamar Hukumar Maigatari da ke Jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar Maigatari ya ce karamar hukumar tana samun Naira miliyan biyu a duk wata a matsayin kudin shiga daga Kasuwar Maigatari. Shugaban karamar hukumar ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Maigatari, inda ya ce yanzu karamar hukumar ta adana Naira […]
Shugaban karamar Hukumar Maigatari da ke Jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar Maigatari ya ce karamar hukumar tana samun Naira miliyan biyu a duk wata a matsayin kudin shiga daga Kasuwar Maigatari.
Shugaban karamar hukumar ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Maigatari, inda ya ce yanzu karamar hukumar ta adana Naira miliyan 16 a matsayin kudin shiga, inda ta kwashi wasu ta aiwatar da muhimman gyare-gyare
a karar shanu da ta awaki da rakuma kuma hakan ya magance rigimar da ake samu a tsakanin dillalan dabobi a kasuwar.
Ya ce a duk mako sama da tirela da roka da motocin kanta 200 ne ake yi wa lodin kayan amfanin gona daga kasuwar Maigatari zuwa sassan kasar nan da wasu sassa na
Afirka.
Ya ce karamar hukumar ta samar da motocin sintiri ga jami’an tsaro don hana yi wa ’yan kasuuwa fashi a kan hanyarsu ta komawa gida daga Kasuwar ta Maigatari.
Game da ayyukan raya kasa ya ce karamar hukumar ta samar da ruwan sha mai tsabta a kauyuka 46 da aka hada wasu da inji yayin da wasu aka hada su da inji mai aiki da hasken rana.
Ya ce karamar hukumar tana samar da ruwan sha ga wasu sassa na kasar Nijar da suka hada da Adare da Ganji saboda tsohuwar dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar.