Kasuwar rigar kwallon Maroko ta bude a Qatar

Muddin kasar ta sami nasara a wasanta da Faransa, bukatar rigar za ta karu sosai

Kasuwar rigar kwallon Maroko ta bude a Qatar

Rigar kwallon Maroko a wani shagon a Qatar

Nasarar da Maroko take samu a Gasar Cin Kofin Duniya ta sa ana rububin rigar kwallon kasar a shagunan sayar da kaya da ke kasuwar Souq Waqif ta Doha, babban birnin Qatar.

Yanzu haka dai an sayar da rigar kasar mai tarin yawa, kuma ana ci gaba da nemanta.

A ’yan kwanakin da suka gabata dai, shagunan kasuwar mai dimbin tarihi sun cire kayayyakin Larabawa na yau da kullum da aka saba gani, inda suka maye gurbinsu da riguna da kuma tutocin kasashen da ke buga gasar.

Magoya bayan kasashen Argentina da Brazil da Qatar mai masaukin baki ne dai aka fi yin cinikin kayansu a makonnin farko na gasar.

To sai dai a yanzu, idon galibin mutane ya koma kan Maroko, wacce a ranar Laraba za ta kece raini da tawagar kasar Faransa.

Wani mai shagon sayar da kaya a kasuwar, Muhammad Sadiq, ya shaida wa gidan talabijin na Aljazeera cewa, “A watan Nuwamba, mukan sayar da rigunan Maroko ’yan kadan daga cikin wadanda muka saro.”

To sai dai ya ce tun lokacin da kasar ta fara taka rawar gani a matakin rukuni, sai bukatar riga da sauran kayan kasar suka karu sosai.

“Duk lokacin da Maroko ta yi nasara a wasanta, sai mun kara saro wasu daruruwan rigunan, kuma duk ranar da za su buga wasansu na gaba, karin rana sun kare,” inji Muhammad Sadiq.

Tun bayan da tawagar dai ta kai wasan dab da na karshe, daruruwan magoya baya suke ta tashi daga wasu kasashen zuwa Doha, daga sassa daban-daban na duniya.

Da zarar sun isa kasar kuma, wajen da suke fara zuwa shi ne kasuwar ta Souq Waqif, kuma abin da suke fara saya da zarar sun je shi ne rigar Maroko ko tutar kasar, ko ma duka biyun.

Anas El-Karim shi ma yana daya daga cikin wadanda suka yi takakkiya daga birnin Berlin na Jamus kwana ɗaya bayan Maroko ta kori Portugal daga gasar.

Idan dai Maroko ta sami nasara a wasanta da Faransa na ranar Laraba dai, dole Muhammad Sadiq da sauran masu shaguna su kara saro kayan kasar da yawa.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos