Kasuwar Sabon Garin na shirin amfani da fasahar sadarwar zamani
An gudanar da wani taro na musamman domin ganin an fara amfani da tsarin fasahar sadarwar zamani ta yadda ’yan kasuwa za su samu damar yin harkokin kasuwanci cikin nasara. Taron wanda ya gudana a Kasuwar Sabon Gari da ke Kano, ya samu halartar shugabannin kasuwar da shugabannin rukuni-rukuni da wakilai daga gwamnatin Jihar Kano […]
An gudanar da wani taro na musamman domin ganin an fara amfani da tsarin fasahar sadarwar zamani ta yadda ’yan kasuwa za su samu damar yin harkokin kasuwanci cikin nasara.
Taron wanda ya gudana a Kasuwar Sabon Gari da ke Kano, ya samu halartar shugabannin kasuwar da shugabannin rukuni-rukuni da wakilai daga gwamnatin Jihar Kano da wakilan hukumar kasuwar da kuma wakilai daga kamfanin da zai samar da hanyar sadarwar, inda aka tattauna al’amuran da suka shafi ci gaban kasuwanci na zamani.
An yi bayanai masu gamsarwa dangane da yadda wannan tsari zai taimaka wa ’yan kasuwar wajen samun kyakkyawan yanayin sadarwa a tsakaninsu da sauran abokan huldarsu na ciki da wajen kasar nan ba tare da samun tsaikon na’urori ba.
Haka an gabatar da tambayoyi ga wakilan kamfanin da zai samar da hanyar sadarwar wato “Broadbased Communication” don samun cikakkun bayanai da alfanun fara wannan shiri na kasuwanci bisa tsarin fasahar sadarwa a kasuwar ta Sabon Gari.
Manyan bakin da suka yi jawabai a wajen taron sun hada da wakilin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Muktar Ibrahim Fagge da wakilin Shugaban Hukumar Kasuwar Sabon Gari, Injiniya Bala dan’azumi da Shugaban Hadaddiyar kungiyar ’Yan Kasuwa ta kasa (AMATA, Alhaji Usaini Gabari kiru da kuma wakilin kabilar Ibo da ke kasuwar, Cif Innocent Ijezie, inda suka nuna gamsuwarsa bisa wannan tunani na fara amfani da fasahar sadarwa wajen bunkasa kasuwanci a kasuwar.
A karshen taron, Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwar Sabon Gari, Alhaji Ado Bilyaminu ya shaida wa Aminiya cewa: “Ko shakka babu idan aka fara aiki da wannan sabuwar fasaha, kasuwanci zai kara inganta sannan kowane dan kasuwa zai fahimci manufofin samar da wannan hanya don ganin harkokin cinikayya sun bunkasa.”
Ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano da Hukumar Kasuwar Sabon Gari saboda kokarin da suke yi wajen kawo managartan hanyoyin bunkasa kasuwanci da cinikayya ta fannoni daban-daban a kasuwannin jihar, tare da tabbatar wa ’yan Kasuwar Sabon Gari cewa wannan shiri zai amfane su sosai idan aka fara aikin da shi.