Kasuwar shanu ta Tulu ta kai shekara 100 da kafuwa – Sarki

Sarkin Kasuwar Shanu ta Tulu da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Mamuda Tulu ya ce kasuwar ta kai shekara 100 da kafuwa. Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a kasuwar. Ya ce tunda aka kafa kasuwar ake kawo shanu, kuma akalla kasuwar ta kai shekara […]

Kasuwar shanu ta Tulu ta kai shekara 100 da kafuwa – Sarki

Alhaji Haruna Mamuda Tulu

Sarkin Kasuwar Shanu ta Tulu da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Mamuda Tulu ya ce kasuwar ta kai shekara 100 da kafuwa. Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a kasuwar.

Ya ce tunda aka kafa kasuwar ake kawo shanu, kuma akalla kasuwar ta kai shekara 100 da kafawa, kuma kakanninsu ne tushen kafa kasuwar.

Ya ce abin da ya sa aka kafa kasuwar shi ne suna kusa da dajin da ya taso tun daga Falgore da ke Jihar Kano ya shigo dajin Lame Burra da ke Bauchi, kuma ya wuce har zuwa Jihar Yobe, kuma dajin ba ya rabuwa da Fulani makiyaya.

Alhaji Haruna Mamuda ya ce kamar shekara biyu da suka gabata, sun samu matsalar rashin tsaro a yankin, ta yadda barayi suka rika damunsu amma yanzu sun gode Allah domin sun samu tsaro. Don haka yanzu Fulani suna nan a gefen yankin, ko ta ina suna zuwa kasuwar.

Ya ce ana kawo shanu zuwa kasuwar a kowane lokaci kuma suna samun masu kawo shanu daga jihohin Bauchi da Kaduna, kuma a kowace ranar kasuwa ana kawo shanu sama da 100.

Ya ce suna samun ’yan kasuwa baki da suke zuwa sayen shanu daga wurare daban-daban kamar Kaduna da Kano da Abuja da Jos da sauran wurare.

Ya ce babbar matsalarsu ita ce Karamar Hukumar Toro ba ta yi musu komai na tallafi ba a kasuwar.

“A yamma da Jihar Bauchi babu kasuwar shanu da ta kai wannan kasuwa. Amma Karamar Hukumar Toro ba ta yi mana komai ba. Sai dai su zo su karbi kudin haraji kawai su fita. Don haka muna rokon karamar hukumar ta gina mana kasuwa ta yi mana runfuna,” inji shi.

Ya ce babu shakka kasuwar tana ba da gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin yankin, domin dubban mutane suna cin abinci ta dalilin kasuwar kuma gwamnati tana karbar kudaden shiga.