Kasuwar WAPA: Yadda uwar kasuwar canji a Nijeriya ta samo asali

Kasuwar WAPA ita ce uwa ga duk kasuwannin canjin kudi, ba a Arewa kadai ba, har a Nijeriya gaba daya.

Kasuwar WAPA: Yadda uwar kasuwar canji a Nijeriya ta samo asali

Kasuwar WAPA kamar yadda aka sani kasuwa ce da ake gudanar da hada-hadar da ta shafi musayar kudaden kasashen waje. 

Kasuwar tana unguwar Fagge a birnin Kano.

Asalin kasuwar WAPA

Duk da dai ba a samu wani bayani game da takaimaimen shekarar da aka fara kasuwanci a kasuwar ba, amma bayanai sun nuna cewa, an shafe sama da shekara 60 ana gudanar da kasuwanci a kasuwar.

Haka kuma bincike ya nuna cewa, wannan kasuwa ita ce uwa ga duk wasu kasuwannin da ake gudanar da canji ba a Arewa kadai ba, har a Nijeriya gaba daya.

Akwai zantuttuka biyu game da yadda aka fara kasuwnacin canji a Kasuwar WAPA, inda wasu ke ganin cewa an fara ne dalilin neman canjin tafiya aikin hajji da zuwan baki daga kasashen da ke makwabtaka da kasar nan.

An ce wasu mutum uku ne suka fara gudanar da harkar canjin kudin a kasuwar, wadda a yanzu kusan mutum 4,000 suke cin abinci a cikinta.

Alhaji Amadu Hudan, wani dattijo ne da ya bayyana cewa, ya taso a cikin harkar domin iyayensu ne suka fara kasuwancin.

A cewarsa kasuwar ta kafu ne yayin da baki masu zuwa fataunci daga kasashen ketare, musamman ma kasar Nijar suke zuwa don yin fatauci, inda suke kawo kayayyakin kasashensu kamar su dabino da cukwi da kanwa da gishiri da sauransu.

Idan sun tashi komawa kasarsu kuma sukan sayi kayayyaki irin namu kamar su rawani Dan Kura da sauransu.

Sai ya kasance a wancan lokaci kasancewar Fagge tana wajen gari kuma daji-daji ne babu gidaje sosai, idan bakin suka zo sai su sauka a unguwar domin akwai wurin da suke daure rakumansu.

Duba da cewa bakin nan suna zuwa da kudaden kasashensu, inda suke bukatar canji da kudaden kasar nan, ya sa wasu daga cikin mutanen unguwar suka fara harkar canja musu kudin kasashensu da namu.

Daga baya da harkoki suka bude sai ya kasance ba kawai kudin kasar nan suke canjawa ba, har da na sauran kasashe, musamman na Afirka ta Yamma.

Haka kuma daga baya har gida guda aka ware ya zama masaukinsu baya ga gidajen abokan cinikinsu da suke sauka.

A cewar Alhaji Hudan, a wancan lokaci masu yin canjin suna kasa kudin ne a kan tabarma karauni.

A nan mai neman canjin zai zo da nasa kudin a lissafa, a ba shi canjin daidai kudinsa ya tafi.

Haka shi ma kudin da aka karba daga wajensa za a juye shi a kan tabarmar.

Idan lokacin iska ne sai a sa duwatsu a danne don kada su tashi.

Babu wata barazana ta tsaro ko tunanin barayi na iya zuwa su yi sata.

Duk da cewa kowa yana sane, masu sana’ar gidajensu suke kai kudin ba banki ba, amma babu wata barazana ta barayi a wancan lokaci kamar a yanzu.

Habakar Kasuwar WAPA

Kamar yadda Alhaji Ahmadu ya shaida mana a baya, lokacin da aka fara harkar canjin ana yi ne a kan tabarma, “To ganin yadda wadancan mutane ke gudanar da harkar canjin kuma ya zama ana samun budi a ciki, sai mutanen unguwar Fagge suka shiga harkar, inda suka fara gudanar da ita a kofar gidajensu,” in ji shi.

Ya ce, da kasuwar ta fara habaka ne sai Alhaji Mamuda Dantata ya bude wani kamfani da yake buge-bugen takardu, kafin daga bisani kuma ya kara habaka da harkar alhazai.

“Kasancewarsa ejen na alhazai, sai ya bude ofishi da ke gudanar da zirga-zirgar alhazai, mai suna West Africa Pilgrims Agency (WAPA), a nan ne aka yi masaukin alhazai da na baki gaba daya wadanda ke zuwa don yin kasuwanci.

“Sannu a hankali sai harkar canji ta rika bunkasa ta yadda mutane da dama suka shigo cikinta,” in ji shi.

Da Aminiya ta tambaye shi ko har yanzu yana gudanar da sana’ar canji sai ya ce, “A gaskiya yanzu saboda shekaru da rauni ba na gudanr da harkar canji, sai dai wasu abokan cinikinmu da suka san mu a harkar, sukan kawo mana harka, sai mu hada su da ’ya’ya da jikokinmu da suke yin sana’ar, idan an yi abin da aka yi mu kuma a ba mu namu kason.”

A cewarsa yanzu kusan kowane gida da ke cikin kwaryar kasuwar ko yake makwabtaka da kasuwar to za a iske dansu ko jikansu na gudanar da sana’ar canji.

Haruna Musa Adamu shi ne Sakataren Kungiyar ’Yan Canji ta Jihar Kano, ya shaida wa Aminiya cewa, tun daga lokacin da sana’ar canji ta kafu a Kasuwar WAPA ake ta samun canje-canje.

Fadadar harkar canji

“Kamar yadda labari ya iske mu an fara wannan sana’a a bakin titin unguwar nan har aka dawo mutane suna yi a kofar gidajensu, inda ake kasa kudaden canjin a kan tabarma.

“Bayan Gwamnatin Kano ta bude Tashar Kuka da ke Kofar Ruwa, sai ya zama nan ne wurin da bakin suke sauka, daga nan kuma sai su kwararo, su shigo Fagge, su canza kudaden da suke da su.

“To daga baya sai mutane suka fara amfani da shagunan da ke jikin gidajensu suna zama a ciki don yin wannan kasuwanci.

Gwamnatin sojin Buhari ta haramta harkar canji

“Ana nan ana wannan harkar har zuwa 1984 lokacin mulkin soja na Janar Muhammadu Buhari, wanda ya nuna cewa bai yarda da harkar ba kwatakwata.

“Maimakon ya kawo musu mafita sai ya haramta harkar gaba daya.

“Aka rika bi ana kama su. Idan ma mutum yana gudanr da harkar da ya ga masu kamen ko Dalar Amurka ce a hannunsa, to zai yar a kasa ya kama gabansa.

“Haka masu gudanar da wannan harka ta canji suka zauna har lokacin da aka samu canjin gwamnati.

Shigowar gwamnati harkar canji

“Da Shugaban Kasa Janar Babangida ya zo sai ya ce ba korar su za a yi ba, gyara za a yi wa harkar.

“Don haka sai gwamnatin ta bayar da damar yin rajista tare da lasisin gudanar da harkar cikin tsari.

“A nan gwamnati ta ba su umarnin komawa tsarin da sauran kasashen duniya suke kai na Kasuwar Shinku (Bureau de change).

“Bayan masu sana’ar sun yi rajista sun ci gaba da harkokinsu, sai suka yi kungiya a tsakaninsu mai suna AL’AMANAT Bureau de Cahnge da GASKIYA.

“To kasancewar ita gwamnati tana samun Dalar Amurka saboda hada-hadar man fetur sai ta dauki matakin bayar da wannan Dala ga ’yan canji.

“A duk mako tana ba su Dalar Amurka miliyan daya, sai su sa Naira a banki kafin mako ta kare sai a kawo Dala a ba su.

“Su kuma sai su zo su zauna su karkasa wannan Dala a tsakaninsu.

“A wancan lokaci kasancewar akwai karancin kudi a hannun mutane, wannan Dala miliyan daya mutum daya ba zai iya fito da canjinta ba, dole sai an taru mutane da yawa sannan za a iya yin canjin,” in ji shi.

Saukaka harkar canji

Ya ce, “Ana nan sai gwamnati ta kara buda harkar, inda ta bayar da dama ga sauran masu harkar canji su yi rajista a karkashin kamfani guda mai dauke da mambobi shida ko bakwai.

“A nan ne kuma gwamantin ta rika ba kowane kamfani Dalar Amurka dubu 50.

“Haka kuma kowane kamfani sai ya mallaki jarin Naira miliyan 10.

“Daga baya kuma sai gwamnati ta ce tana fuskantar karancin Dalar don haka ba za ta iya ba su Dala dubu 50 ba, sai dai za ta bayar da Dalar Amurka Dubu 15 da sharadin kowane kamfani ya sa jarin Naira miliyan 10 zuwa miliyan 35.

“Wannan lamari ya haifar da tsaiko ga harkar canji, inda aka cin gaba da harka wadanda suka cika ka’idar,” in ji shi.

Ya ce, lokacin mulkin Buhari karo na biyu, sai ya sa Bankin CBN ya daina ba ’yan canji Dala gaba daya.

“Wannan matsalar ita ce ta haifar da halin da kasar nan ke ciki na tabarbarewar tattalin arziki.

“Haka kuma shi ya jawo Dalar ke tashin gwaron zabo a kullum.

“Domin gwamnati ta bar ’yan kasuwa su nemo Dalar da kansu don haka idan suka je nemowa sai farashin da mai Dalar ya bayar.

“Haka za su saya komai tsadarta, kin ga kuma idan sun sayo su ma sai sun dora tasu ribar a kai,” in ji shi.

Ya ce, “Kasancewar Dalar Amurka ta zama ruhin canji domin duk kasashen duniya da ita suke amfani ya jawo take shafar sauran kudaden duniya.”

Gudunmawar WAPA ga tattalin arzikin Kano

Ya kara da cewa, Kasuwar WAPA ta taimaka wajen habakar tattalin arzikin Jihar Kano ta hanyar sama wa dimbin matasa aikin yi.

“A yanzu a kasuwar nan muna da mutane wadanda mafi yawansu matasa ne da suka kusa kaiwa 4,000,” in ji shi.

Duk da cewa kasuwar tana tsakiyar gidajen mutane a unguwar, amma ’yan kasuwar sun fi son ta ci gaba da dorewa a wannan wuri.

“Idan kin duba kasuwar a cikin gidajen mutane take domin har a yanzu wasu shagunan a jikin gida suke kuma za a tarar gidan da matan aure a ciki.

“Sai dai yanzu ana ta saye gidajen, ana mayar da su shaguna.

“Mu dai mun fi so mu zauna a nan domin a nan ne aka san masu canji suke, kuma duk da cewa kasuwarmu ba a kewaye take ba, mun tanadi jami’an tsaro da ke yi mana gadi a kasuwar dare da rana.

“Muna bude kasuwa daga karfe 10 na safe kuma muna rufewa karfe 8 na dare.

“Idan aka ga mutum a kasuwa sabanin wannan lokaci, to sai ya yi wa jami’an tsaron bayani,” in ji shi.

Yadda za a magance tashin Dala

Da yake bayar da shawarwari ga gwamnati game da tashin farashin da Dala ke yi, Sakataren ya ce, “Ni a ganina maimakon gwamnati ta hana shigo da Dala daga kasashen waje ko ta kayyade yawan Dalar da mutum zai shigo da ita, kamata ya yi ta sa doka mai karfi wajen tantance yadda mutum ya samo Dalar da sauransu.

“Wannan zai sa ta wadatu, idan ta yi yawa a hannun mutane dole ne farashinta ya sauka.

“Idan farashinta ya sauka kuma dole ne kayayyaki za su yi sauki.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano