Kasuwar zawarawa na ci a Kamaru
A lokacin da Majalisar dinkin Duniya ta ware ranar 23 ga watan Yuni a matsayin ranar bikin tunawa da matan da mazajensu suka mutu, a birnin Maroua na lardin Arewa-mai-Nisa a Kamaru, kowace ranar Lahadi ne aka ware domin cin kasuwar da ke hada kan zawarawa da kuma matan da suka yi wa mazajensu takaba […]
A lokacin da Majalisar dinkin Duniya ta ware ranar 23 ga watan Yuni a matsayin ranar bikin tunawa da matan da mazajensu suka mutu, a birnin Maroua na lardin Arewa-mai-Nisa a Kamaru, kowace ranar Lahadi ne aka ware domin cin kasuwar da ke hada kan zawarawa da kuma matan da suka yi wa mazajensu takaba sakamakon rasa su da suka yi.
Dandalin da ake irin wannan haduwar ita ce kasuwar Founangue, inda daruruwan matan suke fitowa dauke da kayayyakin sayarwa wadanda akasari kayan sutura ne da kuma na adon daki domin su sayar wa mabukata.
Ana cewa dai wadannan mata suna kwashe yini guda ne domin su samu abin da za su saka a bakin salati da kuma abin da za su bai wa kansu da kuma ’ya’yansu.
Daga cikin matan akwai masu ’yan mata da kuma dattawa. Sai dai kuma duk wadda aka ganta a wannan kasuwa dauke da wani abin sayarwa mallakinta alama ce na nuna cewa tana cikin wani matsanancin hali na rayuwa. Saboda haka baya ga kayan sutura ana ganin wadannan mata suna sayar da kwanuka wadanda aka riga aka yi amfani da su, da kuma sabbi. Sai tukwanen girki, da kuma wasu na’urori da suka mallaka.
Ana yi wa kasuwar Founangue lakabi da Kasuwar Zawarawa da kuma matan da mazajensu suka mutu a dalilin cewa daukacin kayan da matan suke kasuwanci a nan daga cikin laifen da aka yi musu suke cirowa su kai kasuwa. Wasu na ganin cewa matan na yin haka ne domin ba su ilimantu ba ta wani fanni ballantana su samu hanyar dogaro da kai. Wadanda mazajensu suka mutu kuma mai yiwuwa ba masu hali ba ne a lokacin da suke raye balle su bar musu wasu kadarori ko kuma arzikin da za su ci moriyarsa bayan ba su.
Har ila yau, wasu na zaton cewa wadanda mazajensu suka sake su, mai yiwuwa suna ganin cewa har idan sun sake yin wani auren, bai kamata su tafi gidan sabon miji da kayan da suka yi amfani da su a gidan tsohon miji ba. Kodayake, wasu yin kasuwancin ya zame musu dole domin tankiyar da ke bijirowa tsakanin dangin miji bayan ya mutu da kuma matar dan uwa kan gado. A lokuta da dama ana zargin dangin miji da gallaza wa matan da aka bari a kan arzikin da dan uwansu ya bari. Wani lokaci su kwace, wani lokaci kuma su nemi da a yi raba-daidai da su bisa ga hujjar cewa akwai wani kaso daga cikin dukiyar tasa da na dangi ne da ba a raba ba.
Sai dai kuma ana samun kayan sayarwa da sauki a wannan kasuwa ta Founangue a farashin da ba kasafai ake samu a wasu wurare ba masamman ma abin da ya danganci sabbin kaya.