Kata-katar da ke naman kassara ilimi a Bauchi

Lokacin da mulki ya dawo hannun farar hula a 1999, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya fito fili ya rika kukan yadda harkokin ilimi suka tabarbare a jihar. daya daga cikin misalin da ya rika bayarwa shi ne akwai shekarar da dalibai takwas ne kacal daga jihar suka ci jarrabawar kammala sakandare […]

Kata-katar da ke naman kassara ilimi a Bauchi

Malam Isa Yuguda Gwaman Jihar BauchiLokacin da mulki ya dawo hannun farar hula a 1999, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya fito fili ya rika kukan yadda harkokin ilimi suka tabarbare a jihar. daya daga cikin misalin da ya rika bayarwa shi ne akwai shekarar da dalibai takwas ne kacal daga jihar suka ci jarrabawar kammala sakandare da za ta ba su damar shiga jami’a ko wata babbar makaranta a daukacin jihar. Saboda haka ya fara aza tubalin farfado da ilimi ta hanyar gyara makarantun firamare da giggina sababbi da kuma tabo makarantun gaba da firamare zuwa sama.
Bayan jyuin juya-halin da ya kawar da mulkin Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi a zaben shekarar 2007, al’ummar jihar sun fara zuba ruwa a kasa suna sha ganin yadda gwamnatin ANPP ta Malam Isa Yuguda a wancan lokaci ta tsunduma ga gyare-gyaren makarantu, inda bayanai suka nuna cikin shekara daya ta farko ta gwamnatin ta gyara fiye da makarantu 30 a sassan jihar wadanda rabonsu da ganin irin wannan gyara an haura shekara 15 zuwa 20 ko ma ba a taba yi musu irin haka ba.
Kwalejin Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci ta A.D Rufa’i da ke Misau kacokan aka rufe ta na tsawon wata shida domin sake mata fasali. Baya ga gyara makarantu, gwamnatin ta kuma gina jami’a mallakar jihar da sauran ayyuka na inganta bangaren ilimin ciki har da kara wa malamai alawus da kara musu girma da sauransu.
Sai dai kash, wannan yunkuri ga alama ana tufka gaba ne baya na warwarewa, sakamakon yadda wasu abubuwa marasa dadi suke aukuwa, kuma an kasa tsayawa a magance su saboda ko dai masu haddasa su ’yan gata ne da ba su iya tabuwa ko kuma siyasa ta shigo cikin lamarin.
daya daga cikin matsalolin da aka fara samu shi ne na zabtare karin alawus din malaman sakandare da na firamare da gwamnatin Yuguda ta yi, wannan ya jawo takaddamar da ta kai ga shiga yajin aiki. Kuma maimakon a yi kokarin nemo maslaha sai jami’an da suke tafiyar da harkokin ilimi a jihar suka dagula al’amarin ta hanyar korar malaman firamare da na kananan makarantun sakandare har dubu uku! Yau da nake wannan rubutu kimanin wata takwas ke nan ba a biya malaman albashi ba, duk da cewa an ce an dawo da wasu bakin aiki. An rika shiryar wa malaman jarrabawa da sunan tantance su kafin a mayar da su bakin aiki, yanzu haka akwai sauran kashi na karshe da aka yi musu jarrabawar da ba a san makomarsu ba.
Ina ganin  yadda al’amura suka dagule a bangaren ilimin ne ya sa a makon jiya Majalisar Jihar Bauchi ta ba da odar a sauke Kwamishinan Ilimi na Jihar Malam Ibrahim Mohammed Aminu. Majalisar bayan sauraren wani kudiri da dayyabu Chiroma daga mazaba Darazau da ya zargi kwamishinan da gazawa ta amince a rubuta wa Gwamna Yuguda takardar neman a sallami kwamishinan.
Sai dai abin tambaya kwamishinan ne matsalar bangaren ilimin ko yaya. Me ya sa majalisar ta kawar da kai daga Shugaban Hukumar Ilimi Bai-daya (SUBEB) ta jihar hukumar da ita ce ta fi dagula harkar ilimi a jihar fiye da ma’aikatar ilimin. Abin da ya sa na ce haka, shi ne shugaban Hukumar SUBEB din Abdullahi Dabo ya zama wani karamin gwamna a jihar ta yadda ba a iya sauyawa ko kalubalantar duk matakin da ya dauka. Misali lokacin da ya sallami malaman firamare dubu uku, an yi ta koke-koken cewa ba a bi ka’ida ba wajen daukar wannan mataki, kuma majalisar da manyan jihar sun yi ta kokari domin ganin lamarin bai abarbarewa ba, amma ya toshe kunnensa ya aiwatar da wannan gurguwar shawara. Akwai bayanan da suke cewa Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya aika  sau uku shugaban ya zo, amma ya ki, ganin haka Sarkin ya tashi da kansa zuwa ofishin hukumar, amma shugaban ya zille ya guje masa. Wannan shi ne irin bayanan da yake yawo a garin Bauchi. Malaman da aka sallama daga aiki laifinsu ba shi ne na rashin kwarewa ba, kamar yadda Hukumar SUBEB ta jihar ke kokarin nuna wa duniya. Bincike ya nuna laifinsu shi ne an nemi su koma bakin aiki bayan yajin aikin da suka shiga, su kuma sun ki saboda kungiyarsu ba ta umarce su da komawa ba.
Wannan kata-kata ce take neman kassara ilimi a jihar a yanzu, kuma hakan na faruwa ne saboda shugaban Hukumar SUBEB din bai tabuwa sakamakon dangantakarsa da Gwamna Yuguda na kasancewa mahaifiyarsu daya.
Don haka bai kamata majalisa ta kawar da idonta daga ainihin abin da ke kasa ba, ta koma kan kwamishina wanda makarantun da suke karkashinsa wato makarantun sakandare da manan cibiyoyin ilimi na jihar suna aiki, an riga an warware ko an kwatar da kurar da ta taso musu.
Idan majalisa ta nemi a sallami kwamishinan ne saboda ya gaza daukar mataki a kan matsalolin da Hukumar SUBEB ta jawo, ina son in shaida maa cewa ba yadda za a yi Kwamishina Ibrahim Mohammed Aminu ya hukunta Alhaji Abdullahi Dabo, dan Moyin Bauchi, saboda dan Moyin Gwamna ne, kanensa ne, kuma shi ya nada shi a kan wannan mukami ba kwamshina ba.        
Ban ce kwamishina a matsayinsa na jagoran harkokin ilimi a jihar ba ya da inda ya gaza ba, amma hakikanin abin da ake fuskanta a yanzu ba gazawarsa ba ce. Gazawa ce ta gwamnatin Malam Isa Yuguda ciki har da su kansu ’yan majalisar. Gwamna dai ba ya zama a jihar, kuma ya bar wakilan da ya nada su tafiyar da harkokin jihar suna yin abubuwan da suka ga dama, jama’a na gani. An yi korafi a kan haka an gaji, amsar Gwamnan ita ce ba a zabe shi domin ya zauna a Bauchi ba,. Ita kuma majalisa ta kasa nuna masa cewa zamansa a Bauchi  yana da matukar muhimmanci domin ganin idonsa zai sa masu sakaci da aiki su gyara zama. Yanzu dai ‘ya’yan talakawa da suke karatu a makarantun gwamnati ne suke zaman dirshan a gida ko suke kara-kainan zuwa makaranta babu malaman da za su koyar da su?
Tambayar da zan yyi wa Majalisar Jihar Bauchi ita ce tana ina aka dauki tsawon wata bakwai ko fiye da sunan tantace malamai ko ba a bian malaman albashi ba ta dauki mataki a kan Hukumar SUBEB ba, sai ta koma tana neman a kori kwamishina?
Ni Gizago ina nan na hajar mujiya domin in ga ko Gwamna Yuguda zai kori kwamishinan ya bar kanensa wanda shi ne kanwa uwar wajen kokarin kassara ilimi a jiharsa! Ina da bayanan da zan zazzage, amma sai in na ga ba a dauki matakin da ya dace ba.