Katanga ta kashe yara 5 a Maiduguri
Yanzu haka rundunar na gudanar da bincike domin gano musababbin abin da ya haddasa rushewar katangar.
Hedikwatar ’yan sanda da ke Maiduguri
Katangar wani gida da ta rushe a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, ta kashe yara biyar, yayin da yaro ɗaya ya ji munanan rauni.
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ta tabbatar da faruwar lamarin.
- Mangal ya yi wa mutum 18,000 aikin ido kyauta a Katsina
- Kashe-kashe da garkuwa da mutane sun dawo a Katsina
Ta ce yaron da ya ji rauni yana karɓar magani a yanzu, yayin da aka fara bincike kan musabbabin rushewar.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Daso, ya ce rundunar ta samu rahoton faruwar lamarin da misalin ƙarfe 8 na daren ranar Lahadi ta hannun jami’in ’yan sandan da ke kula da sashen Bulumkutu.
“Da misalin ƙarfe 8 na dare, mun samu rahoto daga jami’in ’yan sandan sashen Bulumkutu cewa wata katanga ta faɗa kan yara shida,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa biyar daga cikin waɗanda abin ya shafa, waɗanda duk ba su kai shekaru 16 ba, sun mutu nan take.
Yaro na shida daga cikinsu ya samu raunuka kuma ana kula da shi a Asibitin Ƙwararru da ke Maiduguri.
“Aiki na farko da rundunar ta yi shi ne fara bincike nan kan musababbin rushewar ginin da abin da ya shafi yanayin da yaran da al’ummar Bulumkutu ke ciki,” in ji shi.
Ya ce suna son gano abin da ya haddasa faruwar lamarin.
ASP Daso, ya yi kira ga jama’a da su bi ƙa’idojin gini tare da shawartar iyaye da suke sanya ido a kan yaransu.