Katin shaida ga ’yan Arewa: CLO ta maka gwamnatin Enugu a kotu
kungiyar kare hakkin dan Adam (Cibil liberty organization) ta maka gwamnatin jihar Enugu a gaban babban kotun tarayya da ke Enugu a sakamakon zargin tursasa wa ‘yan asalin arewacin Nijeriya mazauna jihar da ta yi domin su yi katin shaida don zama a jihar su gudanar da harkokinsu. kungiyar ta CLO ta kuma bukaci kotun ta […]

kungiyar kare hakkin dan Adam (Cibil liberty organization) ta maka gwamnatin jihar Enugu a gaban babban kotun tarayya da ke Enugu a sakamakon zargin tursasa wa ‘yan asalin arewacin Nijeriya mazauna jihar da ta yi domin su yi katin shaida don zama a jihar su gudanar da harkokinsu.
kungiyar ta CLO ta kuma bukaci kotun ta tilasta wa gwamnatin jihar ta biya ‘yan arewan kudi Naira miliyan dubu hamsin a matsayin diyyar tauye musu hakkinsu na dan Adam.
Bayan kammala zaman kotun a karo na farko, Mista Olu Omotaye, shugaban shiyyar kudu maso gabas na kungiyar CLO, ya yi wa Aminiya karin haske game da lamarin, inda ya nuna cewa, “a wannan shari’a mun kai karar babban lauyan gwamnati da kuma Alhaji Ahmed Garba Turaki mai bai wa gwamnan Enugu shawara ta musamman kan harkokin al’umomi mazauna jihar da Alhaji Haruna sarkin hausawan Enugu da Alhaji Yusuf Sambo , sauran sune Alhaji Tijjani da Alhaji Baba Ali, domin kotu ta bayyana mana ko tilasta wa ‘yan Arewa yin rajista da kuma karbar katin zama a jihar ya dace da kundin tsarin mulki da kuma doka? Domin muna ganin ware ‘yan Arewa da tilasta musu su yi rajista, mazansu da matansu ya keta musu ‘yanci a matsayinsu na ‘yan kasa.”
Ya ci gaba da cewa, “Haka kuma muna neman kotu ta tilasta wa gwamnatin jihar Enugu ta mayar wa ‘yan Arewa kudi Naira miliyan goma sha biyu da rabi da ta karba a hannunsu na rajista.”
BaristA Omotayo ya kara da cewa, sun bukaci kotu ta sanya a biya diyya ne domin hakan ya zama darasi ga duk wani mutum ko kungiya da zai ci zarafin duk wani dan kasa.
Muhammad Lawal, wanda aka fi saninsa da dan Tibi, daya ne daga cikin shugabannin ‘yan Arewa da suka shigar da karar, ya kara wa Aminiya haske game da lamarin, inda ya ce, “ wannan abu hadin baki ne kawai, kuma idan har za su ce sai dan Arewa ya yi katin sana’a to wannan alama ce ta raba kasa, domin idan muma a Arewa gwamnoninmu suka ce za su yi wa kabilarsu haka ai ka ga matsalar da za a shiga ba karama ba ce, don haka mutanen nan ba su yi tunani ba ko kadan.”
Shi ma Musa dan Alkali ya tabbatar da cewa ana karbar kudi, a wani wurin ma har Naira dubu daya da dari biyar ake karba, a wani wurin kuma Naira dubu ake karba a ba mutum takarda.
Akasarin wadanda wakilinmu ya ji ta bakinsu sun nuna cewa sun yi yunkurin su yi katin amma kuma suna yin dari-dari da lamarin yin katin. Duk kokarin da wakilinmu ya yi domin su yi karin bayani ya ci tura, domin suna yin magana ne cikin firgici da tsoro, yayin da wadansu kuma suka tubure suka ce ba za su ce komi ba domin maganar tana gaban kotu.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa, shugabannin da aka kai kara sune ake zargi da hada baki da gwamnati ta sanya a yi katin domin su dadada wa gwamnatin jiha .

Majiyar ta kuma yi zargin cewa, idan gwamnati ta ba da kudi a sayo raguna domin a raba wa al’ummar musulmi mazauna jihar Enugu sai shugabannin su sayo awaki masu arha su raba wa jama’a.
Gwamnatin jihar Enugu dai ta ce ta bullo da yi wa ‘yan Arewar rajista ne domin tantance bara-gurbi a tsakaninsu.
A halin yanzu dai an dage sauraron karar har sai nan da watanni uku masu zuwa, wato ranar 16 ga watan Oktoba mai zuwa.