Katin waya (2)

Wani Bakatsine ne zai tura wa dan uwansa katin waya N1,500 sai aka samu matsala ya tura a lambar wayar wani Bahadeje. Shi kuma Bahadeje yana ganin kati sai ya yi sauri ya saka a wayarsa. Ana ta kiran shi, ana rokon ya dawo da katin amma ya ki daga wayar. Da Bakatsine ya yi, […]

Katin waya (2)
Katin waya (2)

Wani Bakatsine ne zai tura wa dan uwansa katin waya N1,500 sai aka samu matsala ya tura a lambar wayar wani Bahadeje. Shi kuma Bahadeje yana ganin kati sai ya yi sauri ya saka a wayarsa. Ana ta kiran shi, ana rokon ya dawo da katin amma ya ki daga wayar. Da Bakatsine ya yi, ya yi a daga waya, ya ji an ki a dauka sai ya tura tes kamar haka: “Assalamu alaikum dan uwa! Dama ba wani abu ba ne ya sa ka ga na damu da kiranka ba, muna taya ka murna, kana daya daga cikin wadanda aka zaba a matsayin sabbin membobin kungiyarmu ta Boko Haram. Saboda haka ne muka turo maka wannan katin. Ku 500 ne aka zaba kuma duk wanda ya saka katin a wayarsa, alamar cewa ya amsa goron gayyatarmu ke nan, shi ma ya zama namu. Ka saurare mu da sako na gaba, Allah Ya taya riko, amin.”

Bahadeje na ganin sakon nan sai ya yi sauri ya je ya sayo kati na N1,500 guda biyu
ya mayar wa lambar da ta turo masa sakon, ya kara da cewa: “Wallahi dama ban saka katin ba, ga shi nan na maido muku, har ma da karin tallafin wani. Ku tura wa
wadansu. Na gode.”