Katin zabe ne makaminku a kan azzaluman shugabanni – Buhari
Tsohon Shugaban kasa kuma mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan Najeriya musamman magoya bayansa su tabbatar sun samu katin zabe wanda ya bayyana a matsayin makamin da za su yi amfani da shi wajen kawar da azzaluman shugabanni a zaben 2015 mai zuwa. Janar Buhari ya […]
Tsohon Shugaban kasa kuma mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan Najeriya musamman magoya bayansa su tabbatar sun samu katin zabe wanda ya bayyana a matsayin makamin da za su yi amfani da shi wajen kawar da azzaluman shugabanni a zaben 2015 mai zuwa.
Janar Buhari ya ce idan ba su da katin zabe babu yadda za a yi su kawar da jam’iyya mai mulki wato PDP daga mulkin kasar nan.
Tsohon Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da tsohon Ministan Birnin Tarayya, Malam Nasir El-Rufai a matsayin mai neman takarar Gwamnan Jihar Kaduna a filin Kasuwar Duniya da ke Kaduna.
“Kamar yadda sauran masu jawabi suka nemi ku yi katin zabe, ina kira ku tabbatar kun karbi katin zabe da zarar an soma bayarwa saboda idan ba ku da katin zabe komai son da kuke mana ba za ku iya zabenmu ba. Kuma wannan katin zabe shi ne bindigarku ko makamin da za ku yi amfani da shi wajen yakar azzaluman shugabanni a kasar nan. Don haka a tabbatar an samu katin domin zai taimaka muku wajen zaben sanatoci da ’yan majalisa da gwamnoninku har ma da Shugaban kasa,” inji shi.
Janar Buhari, ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kaduna su tabbatar sun zabi Malam Nasiru El-Rufai a matsayin Gwamnan Jihar a zaben 2015.
Ya ce ya daga hannunsa ne saboda ya yarda da irin jajircewarsa da kwatanta gaskiya, musamman idan aka yi la’akari da irin aikin da ya aiwatar a Abuja a matsayinsa na Minista.
Da yake jawabi, Nasir El-Rufai cewa ya yi kafin ya bayyana ra’ayinsa na tsayawa takara sai da ya bi duk masu ruwa-da-tsaki da suka hada da sarakuna da talakawa domin jin ta bakinsu a kan abin da suke bukata a wajen gwamnati.
“Gaskiya na yawatu wajen jin ra’ayoyin jama’a a kan wannan takara tawa. Manufata ita ce in san abin da suke bukata daga gwamnati. Saboda a yanzu Jihar Kaduna na cikin wani matsayi na rashin ci gaba. Makarantu na cikin wani hali, haka fannin kiwon lafiya da sauransu,” inji shi.
Saboda haka ya bukaci jama’a su ba shi goyon baya domin ya samu nasarar canza abubuwa idan ya zama Gwamna, musamman maido da martabar jihar ta hanyar kawo ci gaba mai ma’ana a fannoni daban-daban.