Katinan zabe 200,000 ne ba a karba ba a Adamawa —INEC
Yayin taron manema labarai da ya shirya a Yola ranar Juma’a, Yunusa ya ce sama da katin zabe 200,000 ke zube a ofisoshinsu ba tare da an zo an karba ba.
Yayin da ya rage kasa da kwana 100 kafin babban zaben 2023, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta koka kan yadda jama’a ke kin zuwa karbar katin zabensu.
Sabon Kwamishinan INEC a Jihar Adamawa, Hudu Yunusa, ya nuna damuwarsa kan tarin katin zaben da ke jibge a ofishinsu.
- Matawalle ya rantsar da manyan sakatarori 6
- HOTUNA: Fadar Kano ta marabci Sabon Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda
Ya bayyana wa manema labarai a Yola ranar Juma’a, cewa sama da katin zabe 200,000 ke zube a ofisoshinsu ba tare da an zo an karba ba.
Ya ce katunan na masu zaben da aka yi wa rijista ne tun daga 2019 a tsakanin kananan hukumomi 21 da jihar ke da su.
Jami’in ya ce, an samu karin masu zabe 36,000 da aka yi wa rijista a 2022.
Daga nan, ya bukaci wadanda suka san sun yi rijista amma ba su karbi katin zaben ba, su kokarta su je su karba tun kafin lokaci ya kure.