Katse layukan waya: Zamfarawa da Katsinawa Na Kaura Daga Gida

Jama’a na barin jihohin Zamfara da Katsina don samun damar tuntubar abokan harka

Katse layukan waya: Zamfarawa da Katsinawa Na Kaura Daga Gida

(Hoto: vanguardngr.com


Domin sauke shirin latsa nan.

Kusan mako biyu ke nan tun bayan da gwamnati ta bayar da umarnin katse layukan sadarwa a Jihar Zamfara; kusan mako guda bayan Katsina ta bi sahu.

Ko wanne hali mutanen jihohin ke ciki, musamman ta fuskar mu’amalar kasuwanci, ko zumunci?

Shirin Najeriya a Yau ya tambayi wasu ‘yan asalin yankin yadda suke mu’amala da ‘yan uwa da abokan arziki.