Katsina 2018: Yadda tafiyar Kungiyar Gizago ta faro shekara 10 da suka gabata
A bana ne Kungiyar Gizago ta cika shekara 10 cur da kafuwa. Muhammad Kabir Adam (MK) Gombe (08065432898, 08023281167), Shugaban Kungiyar na kasa ya gabatar da jawabi a babban taronta na kasa da ya gudana a Katsina, ranar Asabar 22/09/2018, kamar haka: Masu girma manyan baki, iyayen kungiya a matakin kasa da jihohi, tsofaffin shugabanni […]
A bana ne Kungiyar Gizago ta cika shekara 10 cur da kafuwa. Muhammad Kabir Adam (MK) Gombe (08065432898, 08023281167), Shugaban Kungiyar na kasa ya gabatar da jawabi a babban taronta na kasa da ya gudana a Katsina, ranar Asabar 22/09/2018, kamar haka:
Masu girma manyan baki, iyayen kungiya a matakin kasa da jihohi, tsofaffin shugabanni a matakin kasa da jihohi; ’yan uwana Gizagawa maza da mata, assalamu alaikum.
A yau cike nake da farin ciki tare da mika godiyata ga Allah (SWT) da Ya kaddari haduwarmu a wannan rana a daidai wannan lokaci, a cikin wannan dakin taro domin sake jaddada zumunci. Baya ga haka, ina muku barka da zuwa wannan taro namu mai cike da dimbin tarihi da albarka ga daukacin Gizagawa.
Babu shakka kamar yadda da yawa daga cikinku suka sani, silar haduwarmu, ya samo asali ne ta cikin jaridar Aminiya a watan Afrilun shekarar 2008, ta dalili jagora kuma mu’assasi Malam Bashir Yahuza Malumfashi.
A lokacin nan muka hadu domin sada zumunci da taimakon juna, daga bisani ’ya’yan kungiyar suka fadada ayyukanta ta fuskar habaka harshen Hausa da inganta al’adun Hausawa da taimaka wa marayu da kai ziyara gidajen yari da kuma auratayya a tsakanin juna.
Da irin wadannan aikace-aikacen ne Kungiyar Gizago ta cika shekara goma a yau. Ko ba a fada ba ka san cewa shekara goma ba mako goma ko wata goma ba ne. Shekara goma, ko a tsakanin ma’aurata ne ka san an yi hakuri da juriya da kuma dauriya, bare kuma a ce a kungiyance, inda aka hada al’umma mabambanta, daga jihohi mabambanta, masu bambancin shekaru suka hadu a cikin inuwar zumunci; inda ra’ayinsu ya zo daya.
A cikin shekara goma da kafuwar Gizago, ta yi shugabanni a matakin guda biyar da suka hada da 1-Alhaji Muttaka Abdul-Hadi Dabo (Zariya). 2-Alhaji Yunus Abdullahi (Kogi). 3-Sharif Auwal Falala (Abuja) 4-Nura Adamu Ahmad (Kano). 5-Sai kuma ni da nake jagorantar kungiyar a yanzu, Muhammad Kabir Adam Gombe.
Hakika an yi hakuri a wurare daban-daban, an kuma samu akasin haka a wasu a lokutan. Ke nan hakan yana nuna mana cewa an cimma nasarori da dama, an kuma amfana da juna ta hanyoyi da dama. Ba zan iya kawo dukan nasarorin ba, kuma hakan ba yana nufin ba zan iya ba ne sai don saboda karancin lokaci amma ga kadan daga cikinsu:
Manyan nasarorin da aka samu tun daga kafuwar kungiyar zuwa yau su ne kamar haka:
1-Ta mallaki takardar rijista da Hukumar Yi wa Kamfanoni da Kungiyoyi Rajista ta Kasa (CAC). 2-Ta bude wa uwar kungiya asusun ajiya da Bankin Diamond.
3-Ta tara kudi domin taimaka wa al’umma da ’yayanta.
4-An kuma yi auratayya a tsakanin juna kuma kadan daga cikinsu, an yi a Kano da Katsina da Kaduna da kuma Sakkwato. Bincike ya tabbatar mana suna nan suna ci gaba da hayayyafa, Allah Ya yi wa zuri’a albarka, amin.
5-Hada huldar kasuwanci da zumunci mai karfi a tsakanin juna, zumuncin da idan na ce mutuwa ce kadai za ta raba ban yi kuskure ba.
Ga nasarorin da mu kuma muka samu a cikin wata 17 da hawanmu shugabanci a ranar Asabar 3/04/2017, a dakin taro na Jam’iar Alkalam a Jihar Katsina, inda nan ne cibiyar kungiyar ke da zama:
Kamawarmu da wata daya muka bude wa uwar kungiya asusun ajiya, wanda tun asali ba ta da shi. (Diamond Bank, Gizago Social And Cultural Association, mai lamba 0089537687). An bude asusun ne da Naira dubu ashirin da dari biyu. Mun yi kananan tarurruka a jihohin Kaduna da Nasarawa, tarurrukan da kundin tsarin mulkin kungiya ya ambata a yi, kafin Babban Taron Kasa, wanda ke gudana a halin yanzu! Kudin ya kama Naira dubu 101 da 520.
Kungiya ta kai kayan tallafi na abinci da kudi kimanin Naira dubu 120 da 175 a gidajen mambobinta uku da suka rasu.
1-Alhaji Usman Gambo Funtuwa Jihar Katsina.
2-Malam Khalid Ladan Birnin Kudu, Jihar Jigawa.
3-Malam Abdulmalik Danbirni Jihar Ondo.
4- Cikon na hudun shi ne Malam Lawal Ahmad Abuja, wanda ya rasu a ranar 10/09/ 2018. Shi ma za mu yi iya yinmu, domin ganin kungiya ta kai wa iyalansa tallafi, insha Allah. A wannan dakin taron gidauniyarmu za ta fara neman taimako daga gare ku, ina fatan za a taimaka Allah, Ya ba da ikon taimakawa.
Sai abin da ya shafi katin waya, zirga-zirga da buga takardu, Naira dubu 47 da 550. Jimlar kudin sun kama Naira dubu 291 da 245.
Abin da ya shigo asusun kungiya kuma Naira dubu 227 da 200, idan aka debe abin da ya shigo daga cikin abin da aka kashe, za a ga an biyo kungiya bashin Naira dubu 64 da 45. Wadannan kudi sun fito ne daga aljihun Shugaba na Kasa.
Hakazalika mun kafa kwamitoci kamar haka:
Kwamitin Sulhu da Maido da Martabar Kungiya da Kwamitin Gidauniyar Marayu da Kwamitin Taron Kasa da Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Kungiya, wanda a yau ake rantsar da ’yan kwamitin, a wannan taro, inda muka ba su wa’adin wata uku.
Game da hanyoyin samun kudin kungiya, kamar yadda aka sani kowace kungiya tana da hanyoyin samun kudin shigarta. Wani abin burgewa da ban sha’awa shi ne, Kungiyar Gizago tana samun kudin shigarta ne ta hannun ’ya’yatanta da iyayenta. Saboda haka muna mika kokon bara ga mahalarta wannan taro mai albarka, in akwai wanda yake da hanyar hada wannan kungiya da manyan kungiyoyin da ke ba kananan kungiyoyi tallafi ko ta fuskar gwamnati, muna bukatar hakan. Ina fatan iyayen kungiya da mahalarta taron za su taimaka wajen duba wannan koke namu.
Daga karshe muna mika godiyarmu da addu’armu ga Uban Kungiya Mai girma Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar (NPOM), Babban Jojin Jihar Katsina, bisa irin gudummawa da kulawar da yake ba kungiya a duk lokacin da muka zo da bukatar kungiya; wanda a wannan taro da ke gudana a halin yanzu shi ya ba da kaso mafi tsoka. Allah Ya kara wa rayuwarsa albarka da lafiya.
Shi ma mu’assasin kungiyar, wanda ta sanadiyyarsa ce muke dabbaka wannan zumunci, muna addu’ar Allah Ya kara wa rayuwarsa albarka, tsawon rai da kuma lafiya. Shi kuma kamfanin Daily Trust mai buga jaridar Aminiya da dukan ma’aikatansa, Allah Ya kara musu daukaka da nagarta, Ya kara wa jagororinsa hakuri da lafiya.
Muna kara godiya ga dukan wanda ya taimaka da kudi ko lokaci, ko shawarwari har wannan taro ya kammala. Allah Ya saka da mafificin alheri, Ya kuma mai da kowa gida lafiya. Muna godiya kwarai da gaske, Allah Ya sake sada fuskokinmu da alheri.