Katsina a shekara 30: Ko an bar baya da kura?

  Bibiyar tarihin kafuwar Jihar Katsina a daidai wannan lokaci da ta cika shekara 30 cur dole ne a tabbatar d anasara da akasinta, ta yadda bayan mun kammala murna da bukukuwa sai mu kara himma wajen tabbatar da managasrtan ayyukan da shugabaninmu suka aiwatar, mu kuma kokarin yin gyara kan duk irin abin da […]

Katsina a shekara 30: Ko an bar baya da kura?
Katsina a shekara 30: Ko an bar baya da kura?

 

Bibiyar tarihin kafuwar Jihar Katsina a daidai wannan lokaci da ta cika shekara 30 cur dole ne a tabbatar d anasara da akasinta, ta yadda bayan mun kammala murna da bukukuwa sai mu kara himma wajen tabbatar da managasrtan ayyukan da shugabaninmu suka aiwatar, mu kuma kokarin yin gyara kan duk irin abin da bai yi daidai ba. Kun ga ken an ba laifi ba ne idan aka ce a yi gyara kana bin da wani gwamna ko wnai jigo a jihar ya yi kuskuren aiwatarwa a daidai lokacin d ayake bisa karagar mulki. Shi ya sa nike ganin babu abin Gwemananmu Dallatun Katsina zai kara kwazo a kai illa yadda za a ci gaba da bunkasa jiharmu, tare d aneman daukacin al’umma su bayar da gudunmuwarsu da kishin jiha da ma kasa baki daya.

Ni dai ina ganin kamata ya yi mu daina duk wani ce-ce-ku-ce, kan ko ana yi da wane ko ba ayi da shi. Domin mulkin nan dai da Allah Ya mika wa bayinSa don su kula harkokin rayuwar al’umma, musamman tabbatar da adalci da kyautata walwala da jin dadin jama’a. Mu daina karon-batta ko taho mu gama kan wata matsala ta masu mulki. Domin ko wane ne yake bisa mulki wata rana zai sauka ya barmu. Saboda haka kokari ya kamata mu yi wajen taimaka wa masu mulki su ji dadin tafiysar da al’amuran rayuwarmu. Mu ba shu shawara tagari, in ma ta kama suka mai ma’ana, amma ba cin mutuncin wani ba. Al’ummar Jihar Katsina mu sha biki lafiya. Allah Ya maimaita mana.

Da  farko  ina mika sakon farin ciki ga daukacin ya’yan asalin jihar Katsina, wacce ta cika shekaru 30 da samun jiha. Kuma ta samu gwamnoni har guda goma cur, wanda hakan darusssa ne  cewa, ‘duk abin da ya yi farko to da sannu zai yi karshe. Anan ina magana ne kan yadda na ga jerin sunaye da aka wallafa na wadanda suka yi gwamna a jihar a wasu shekaru da suka gabata, wanda ni Mukhtar ina daga cikin wadanda suka gamsu, kuma muka yi zamani da su, muka ga aikin kowa da salon irin nashi jagoramcin.

Yau a cikinsu akwai mutum guda ko biyu wadanda suka bar doron duniya sai tarihinsu. Ashe duk wanda zai hau wani matsayi ya dace ya kalli tarihin magabatan shi, inda suka yi abin kwarai ya dora inda aka yi kuskure ya kauce wa hakan. Don haka nike so in jawo hankullan wasu da ke ce-ce-ku-ce a ranar da aka yi taron murna da cikar  Jihar Katsina shekara 30 d akafuwa, wanda Maigirma Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari, Dallatun Katsina ya jagoramta. Baki da ’yan gida zuwa ’yan kallo suka yi hidima aka tashi lafiya a cikin farin ciki. Wanan al’amari ya sanya na hango cewa masu ce-ce-ku-ce na  ganin an yi tuya an manta da albasa, to ko sun mayar da wukarsu kubenta?

Jihar Katsina jiha ce mai tarihin jarumta da rashin tsoro tun shekaru aru-aru, wanda samun akasin hakan illa ce a garemu, a nan duk masu tunani da tsokacin cewa an yi taro babu wani daga cikin tsofaffin gwamnoni to ni a nawa ganin da muguwar rawa ai gara kin tashi. Ko ba haka ba? Wato tabbas idan wancen gwamnan ya shigo taro zai iya samun dimbin magoya baya domin ya riki jihar, kuma ya yi ma wasu daidai haka a jagorancin wannan gwamnati mai kimanin makonni 121 da kwanuka a yau litinin  25/09/2017, kwanukka 850, ina ganin dole ne a samu dimdin magoya bayan Dallatun Katsina, wato gwamna mai ci Alhaji Aminu Bello Masari. Kun ga ke nan za a iya samun taho mu gama ko kuma musayar murya a tsakanin magoya bayan tsohon gwamna da mai karagar mulki a yanzu. Wannan shi ne dan hasashena wanda na ga dacewar tun farko kada mutanen Jihar Katsina su bayar da mu a idon jama’a a taron farin ciki, wanda idan ya yi kyau, to mu muka yi abin yabo, idan aka samu akasi mu ne da nadama. Duka dai fatanmu a kalli irin nasarar da Katsina ta samu tun kafuwarta a shekara ta 1987, wanda ya zuwa yau ta samu wadanda bayan sun riki matsayin gwamna, kuma suka zamo shugabannin kasa, da fatan inda duk wani ko wata daga cikin al’ummar Jihar Katsina suke mu zamo masu kishin jiharmu da taimakonta da addua.

Mukhtar Ibrahim Saulawa Iyalan Ummarun Dallage Dallazawa, buhari gobernment supporter. gsm: 07066434519/08080140820 Mukhtar Ibrahim Saulawa [email protected].