Katsina: Ci gaba ko koma baya?

‘Allah Ya kawo mu, shekara ta kawo mu,’ wannan dai it ace shekarar zabe, don haka nike ganin ya dace in yi kira ga Katsinawa kada su sake su yi zaben tumun dare, musamman ma ganin cewa akwai zabi tsakanin ’yan takarar jam’iyyun APC da PDP da APGA. Kodayake wani ya yi rubutu kan sabon […]

Katsina: Ci gaba ko koma baya?
Katsina: Ci gaba ko koma baya?

‘Allah Ya kawo mu, shekara ta kawo mu,’ wannan dai it ace shekarar zabe, don haka nike ganin ya dace in yi kira ga Katsinawa kada su sake su yi zaben tumun dare, musamman ma ganin cewa akwai zabi tsakanin ’yan takarar jam’iyyun APC da PDP da APGA. Kodayake wani ya yi rubutu kan sabon salon siyasa a Jihar Katsina, inda ya nuna gwarzonsa a matsayin wanda zai kwashi kuri’u, amma bai nuna ayyukan gwarzon nasa ba.

Mu dai mun san nagarta wadannan ’yan takara a siyasance, musamman ma ganin cewa kowanensu ya yi aikin gwamnati, ya kuma tsunduma a harkokin siyasa. Don gudun kada a zabi bara-gurbi, sai mu ce wa Katsina ga Nashuni da Masari da Tata, sai a tantance.
A wannan karni na ci gaba, babu abin da al’umma ke bukata irin kyautatuwar harkokin rayuwa, musamman al’amuran da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki da siyasa. Kuma ba a samun irin wannan ci gaban, sai an samu shugaba nagari, wanda zai dauki kowa a matsayin nashi, ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ko yanki ba.
Gwamna Ibrahim Shehu Shema ya yi rawar gani, kuma al’umma ta yaba kan yadda ya aiwatar da ayyuka a fannonin da suka hda da kiwon lafiya da ilimi da samar da hanyoyin ababen hawa, tare da bunkasa aikin gona. Don haka sai mu bibiyi ’yan takarar neman kujerar gwamna a Katsina, don zakulo wanda zai kwatanta, ya kuma dora a kan ayyukansa.
Aminu Bello Masari dan takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin tutar Jam’iyyar APC, tsohon Shuygabnan Majalisar wakilai ne, kuma tsohon Kwamishinan albarkatun ruwa, wanda a sanina babu wani abu da zai nuna a matsayin aikin da ya yi wa Katsinawa. Kuma babu wasu alamu da ya nuna irin shirin ayyukan da ya tsara idan ya zama gwamna. Shi ma Umar abdullahi Tsauri, dan takarar Gwmana a karkashin tutar jam’iyyar APGA jirgi daya ya kwaso su; sai dai in an yi la;’akari shirin raba kan al’umma da ya yi, ta hanayar amfani da addini don cimma burinsa na siyasa. Hasali ma ya kasa amsa wasu tambayoyi kan yadda zai kyautata rayuwar al’ummar jihar. Domin shi a ganinsa fakewa da addini zai sanya ya samu kuri’un mutane.
kimar sauran ’yan takarar jam’iyyu da aka auna a sikeli, ta sanya Katsinawa ba su da wnai zabi illa su kada kuri’unsu ga Injiniya Musa Nashuni. Domin a cewarsa, matukar aka zabe shi, to, zai mayar da hankalinsa ne kacokan wajen ci gaba da ayyukan gwamnatin Ibrahim Shehu Shema ta aiwatar a fannonin da suka ahda da ilimi da kiwon lafiya da noma da tsaro da bunkasa rayuiwar al’umma.
Idan har Gwmana Shema ya smau nasarar samar da kayan more jin dadin rayuwar al’umma, wadanda suka hada da hanyoyin ababen ahwa 100 da fadada filin jirgin saman Jihar Katsina; ga wutar lantarki a karkara, al’amarin da ya yi tasiri a kan al’ummomi 200, snanman ga gidaje sama da dubu hudu da aka gina a kowace karama hukuma, shin me Katsinawa ke nema in ba wanda zai dora a kan wadannan ayyuka ba?
Lallai akwai bukatar mu kasance masu ra’ayi na kanmu, kada mu bari a yaudare mu. Domin nagartar dan takara it ace abin dubawa. Bayan an tabatar da cancantar mutum sai kawai a yanke cewa ya cancanci a kada masa kuri’a. Katsina sai a yi la’akari da wanda zai ci gaba da aiwatar da ayyukan raya kasa, wadanda za su yi tasirin kyautata rayuwar al’umma.
Ranar zabe dai na karatowa, kuma a wannan rana za a tantance tsakanin tsaba da tsakuwa, a Jihar Katsina da fadin tarayyar kasar nan. To, Katsina kada ku bari wadanda ba su da wani shiri na musamman sai bata lokaci, inda za a shafe shekaru ba gaba, ba baya. Mu dai ci gaba muke fata, amma ba na mai hakar rijiya ba. Don haka wanda duk ya yarda da cewa Gwamna Shema ya aiwatar da ayyukan raya kasa, tabbas zai bukaci a dora daga inda ya tsaya. Saboda haka Katsinawa sai a yi karatun ta-natsu.
Muhammad Bauchi ya rubuto makalarsa ne daga gida Mai lamba 34 Gamji road, Jihar Kaduna kuma za a iya tuntubarsa ta :
[email protected]

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu