Katsina: Sojoji sun ceto wanda aka sace, sun lalata sansanin ’yan bindiga
Samamen wani ɓangare na ƙoƙarin tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda, da katse hanyoyin samar musu da kayan aiki, tare da dawo da tsaro a al’ummomin yankin Arewa maso Yamma
Dakarun sojin Najeriya sun ceto wani mutum mai suna Nura Yar’adua da aka yi garkuwa da shi, tare da lalata wasu maboyar ’yan ta’adda yannkin Karamar Hukumar Mataza ta Jihar Katsina.
A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta katse layin sadarwa tare da haramta sana’ar hada-hadar kudi ta POS da kuma cajin waya da kuma hawa babur a kananan hukumomin Matazu da Musa a yunkurin mahukunta da dakile ayyukan ta’adddanci da kuma toshe hanyoyin da ke taimaka wa ayyukan ’yan ta’adda.
Gwamnatin jihar ta kuma haramta sayar da man fetur a cikin jarka da kuma sana’ar bumburutu a fadin jihar a matsayin wani bangare na wannan mataki wanda ya biyo bayan rasuwar Manjo-Janar Rabe Abubakar (ritaya) a hannun ’yan bindiga da suka garkuwa da shi tare da matarsa a yankin Karamar Hukumar Matazau.
Sojojin Rundunar Operation Clean Sweep sun yi nasarar na a rana ta hudu da suke ci gaba da kai hare-hare a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda, da katse hanyoyin samar musu da kayan aiki, tare da dawo da tsaro a al’ummomin yankin Arewa maso Yamma.
Rundunar sojin ta bayyana cewa ranar Juma’a dakarun sun gudanar da wani samame na haɗin gwiwa kan sansanonin ’yan ta’adda da ke ciki da kewaye da garin Tuga a Ƙaramar Hukumar Matazu.
An gudanar da aikin ne tare da taimakon bayanan sirri na lokaci-lokaci, da na’urorin sa ido da tattara bayanai, baya ga hare-haren sama na musamman da Rundunar Sojin Sama da ke ƙarƙashin Operation Fansan Yamma ta kai.
- Mahafiyar Kachalla Battujo za ta shekara 20 a gidan yari
- Tafiya a saman tirela: Ganganci ko neman sauki?
- An yanke wa mai sayar da tikitin keke Napep hukuncin kisa
Majiyoyin sun ƙara da cewa daga nan ne dakarun suka kutsa cikin dajin Fafu, wanda ya yi ƙaurin suna a matsayin mafakar ’yan ta’adda, a ci gaba da aikin da aka kaddamar mai suna da nufin ‘Relentless Incursion’ da nufin hana ’yan ta’adda samun wuraren fakewa.
Bayan kai hare-haren haɗin gwiwa ta sama da kuma luguden wuta da manyan bindigogi kan wuraren da aka gano, dakarun ƙasa sun shiga yankin inda suka lalata sansanoni da maboyar sirri da ’yan ta’addan ke amfani da su.
A yayin ci gaba da bincike a yankin, rahotanni sun nuna cewa dakarun sun gano wata maboya da ke da alaƙa da wani fitaccen shugaban ’yan ta’adda, inda ake tsare da mutanen da aka yi garkuwa da su cikin mawuyacin hali.
Hukumomin soji sun ce an gano gawarwakin mutane biyu a wurin, yayin da aka tarar da wani mai suna Nura Yar’adua cikin sarƙoƙi, suka ceto shi.
Rundunar sojin ta ƙara da cewa an ba shi agajin gaggawa kafin a kai shi Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina domin ci gaba da kula da lafiyarsa.
Har ila yau, dakarun sun ƙwato shanu 36 da tumaki 280 da jakuna biyu da ake zargin ’yan ta’addan sun sace.