Katsinawa sun kadu bayan ’yan bindiga sun fara amfani da wayar oba-oba
Jama’a na zargin matakin da gwamnati ta dauka bai yi tasirin komai ba, sai kara jefa su cikin mawuyacin hali.
Bayan rufe layukan wayar da Gwamnatin Jihar Katsina ta yi a kananan hukumomin da suke fama da matsalar hare-haren ’yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa gami da kisan ba gaira babu dalili, rahotanni sun bayya cewa, ’yan bindigar na amfani da na’urar sadarwar nan ta “Walkie-Talkie” ko ‘Oba-Oba.’ domin yin mu’amulla a tsakanin su.
Lamarin ya kara jefa jama’a cikin tunani cewa matakin da gwamnati ta dauka bai yi tasirin komai ba, sai kara jefa su cikin mawuyacin hali.
- ’Yan bindiga: Tsaka-mai-wuyar da masu shiga tsakani da ba jami’an tsaro bayanai ke ciki
- Buhari ya dukufa wajen fitar da ’yan Najeriya daga talauci —Sadiya
Ga dai karin hare-haren da ake samu kusan kullum sannan babu wata hanyar da za su nemi wani dauki daga jami’an tsaro ko makwabta.
Sai dai na’urar ba mai cin dogon zango ba ce kamar yadda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustafa Inuwa tare da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Sanusi Buba suka shaida wa manema labarai a gidan gwamnatin jihar.
Dukkansu sun bayyana cewa, lallai ana da wannan labarin kuma jami’an tsaro na nan sun dukufa tare da masana domin ganin cewa sun hana ’yan ta’addan yin amfani da wannan na’ura wadda ake zargin wasu bata-gari ne ke samar musu ita ko kuma ta hanyar saye ta intanet.
Mustafa ya ce an kira taron na manema labarai ne domin kara yi wa al’ummar Jihar Katsina bayani a kan dokokin wucin gadin da aka kafa domin dakile ayyukan ta’addancin da ake yi a wasu sassan jihar.
A cewarsa, tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu duk kuwa da halin kuncin da jama’a suke fuskanta wanda ya ce sai an yi hakuri kafin ganin an samu nasara a kai.
“Kadan daga cikin irin nasarorin da wannan dokar ta samar sun hada da hana samun bayanai daga masu ba su labari a kan inda za su kawo hari ko shigar jami’an tsaro domin kai musu farmaki.
“Kazalika, an hana barayin shanun samun damar sayarwa a kasuwanni wanda ya rage musu samun hanyar kudade.
“Yin garkuwa da mutane ya yi sauki fiye da baya; Dokar ta rage yawan kwacen babura da kuma shigar musu da man fetur da suke amfani da shi suna zubawa ababen hawansu.”
Sakataren gwamnatin ya kara da cewa, idan aka lura daga lokacin kafa dokar zuwa yau, misali a tsakanin watan Yuli da Agusta na 2021 an samu rahotannin yin garkuwa da mutane har 173 wanda ya shafi mutane 475.
Amma a tsakanin watan Satumba da Oktobar 2021 an samu rahoton garkuwa da mutanen sau 61 wanda ya shafi mutane 102.
Sakataren gwamnatin wanda ya tabbatar da cewa a yanzu maharan sun fi kai hare-harensu a yankin Faskari, musamman a can kan iyaka da Jihar Zamfara, yankin da ke fama da hare-haren Adamu Aliero, shahararren dan bindigar nan wanda hukumar ’yan sanda ta sanya ladar Naira milyan uku ga duk wanda ya kawo shi da rai ko a mace ko ya yi sanadiyar kama shi.
Ya ce ana alakanta hare-haren da ramuwar gayya daga ’yan bindigar sabod ’yan sa-kai da ke kai wa rugagen da ba su ji ba su gani ba hari, ko idan suka ga Bafillace a kasuwa.
Su ‘yan sa-kan suna lullube fuskokinsu a duk lokacin da za su kai irin wannan hari da kan janyo martanin Fulanin a kan duk wani mai tsautsayi.
A karshe Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar, CP Sanusi Buba, ya kara yin kira ga jama’a da su ci gaba da tona asirin duk wani bata-gari, musamman irin masu gidajen man da ke sayar wa masu kai wa barayin daji da sauran masu taimaka wa ayyukan ta’addanci.