Gwamnatin Katsina Ta Sayo Motoci Masu Sulke Don Yaƙar ‘Yan Bindiga

An kaddamar da motocin yaƙin da za a girke su a yankunan da ’yan ta’adda suka addaba

Gwamnatin Katsina Ta Sayo Motoci Masu Sulke Don Yaƙar ‘Yan Bindiga

Gwamna Dikko Radda ya kaddamar da motoci masu sulke 10 domin yaki da ’yan bindiga da sauran masu tada kayar baya a Jihar Katsina.

Kamfanin Dillancin aLabarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito a yayin kaddamar da motocin ranar Litinin, Dikko Radda ya ce, za a raba motocin ne ga jami’an tsaron hadin gwiwa a jihar domin yakar ’yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Ya bayyana cewa, za a kai motocin ne kananan hukumomi takwas da ’yan bindiga suka hana su sakat.

Kananan hukumomin sun hada da Safana da Batsari da Danmusa da Kankara.

Sai kuma Faskari, Sabuwa da Dandume da Jibia.

Ya ce, “Gwamnati ta kuduri aniyar kawar da ’yan bindiga da masu aikata miyagun laifuka a jihar Katsina.”

Radda ya kara da cewa, an samu nasarori da dama tun bayan fara aikin rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jihar.

Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, inda ya bayar da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da ba su tallafin da ya dace domin dawo da zaman lafiya a fadin jihar.

Gwamnan ya bukaci jama’ar jihar su rika taimaka wa jami’an tsaro da sahihan bayanai dangane da masu aikata miyagun laifuka a yankunansu a kan kari.

A nasa jawabin, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dokta Nasiru Muazu-Danmusa, ya ce samar da motoci masu sulke ya nuna aniyar gwamnati na kare jama’a.

Ya ce, gwamnati za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro domin kare al’umma da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

A nasa jawabin,  mataimakin kwamishinan ’yan sanda Ibrahim Saad, ya yaba wa gwamnati bisa samar da motocin, ya kuma yi alkawarin cewa za a raba su yadda ya kamata domin murkushe ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka.