Katsina: ’Yan Bindiga sun gindaya sharuddan dakatar da kai hari
’Yan bindigar da ke kai harehare a jihar Katsina da kewaye sun gindaya sharuddan aje makamai da kai hari, inda suka bukaci a saki ‘yan uwan su da aka tsare a wasu gidajen yari. Sannan sun bukaci jami’an tsaro da sarakunan da alkalan unguwanni da su taimaka wajen nemo masu dabbobin su. A yayin tattaunawar […]
’Yan bindigar da ke kai harehare a jihar Katsina da kewaye sun gindaya sharuddan aje makamai da kai hari, inda suka bukaci a saki ‘yan uwan su da aka tsare a wasu gidajen yari. Sannan sun bukaci jami’an tsaro da sarakunan da alkalan unguwanni da su taimaka wajen nemo masu dabbobin su.
A yayin tattaunawar da Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, ya yi a kauyen Dankolo da wasu da suke cikin ‘yan bindigar sun ce, jama’ar unguwanni da masu unguwanni da alkalai ne suka tunzura su shiga wannan mummunan aiki da suke yi.
Daya daga cikin ‘yan bindigar mai suna Idris Yayande, ya ce ”Muna da namu korafin saboda an tsare ‘yan uwanmu da dama kamar su Alhaji Baldu, Alhaji Lawal da Ibrahim Nakutama, wadanda aka kama su daga dawowar su aikin Hajji. Sannan ni kaina har yanzu an tsare ni ba a sanar da ni laifina ba. An taba tsare ni na wata 15 kafin a sako ni. “