Katsinawa da suka kammala digiri da daraja ta farko za su samu aiki kai tsaye — Radda

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta biya dukkan bashin tallafin karatu na ɗalibai daga shekarar 2021 zuwa 2026.

Katsinawa da suka kammala digiri da daraja ta farko za su samu aiki kai tsaye — Radda

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da cewa za ta riƙa ɗaukar ’yan asalin jihar da suka kammala karatu da digiri mai daraja ta farko aiki kai tsaye a ma’aikatun gwamnati.

Gwamna Dikko Umaru Radda ne ya bayyana hakan yayin rufe taron Makon Ɗaliban Katsina karo na farko da aka gudanar a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Radda ya ce a baya tsarin ya taƙaita ne ga waɗanda suka yi karatu a manyan makarantu da ke cikin Katsina, amma yanzu an faɗaɗa shi zuwa dukkan ’yan asalin jihar da suka samu digirin mai daraja ta farko daga kowace makaranta da aka tabbatar da sahihanci a Najeriya.

A cewarsa, manufar ita ce ƙarfafa wa ma’aikatun gwamnati da ƙwararrun matasa da kuma ƙarfafa gwiwar ɗalibai wajen yin ƙwazo a karatu.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta biya dukkan bashin tallafin karatu na ɗalibai daga shekarar 2021 zuwa 2026.

Ɗalibai da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi sun yaba da matakin, suna mai cewa zai ƙara wa matasa himma wajen neman ilimi.