Katsinawa: Ina magajin Gwamna Shema?
daukacin Katsinawa sun san cewa Gwamna Ibrahim Shehu Shema ya bayar da muhimmiyar gudunmuwa wajen raya Jihar Katsina, a tsawon mulkinsa na shekara takwas, musamman in an yi la’akari da asibitoci da makarantun da ya raya. Don haka duk wanda zai gaji Shema a Jihar Katsina yana da matukar alfanu ga al’umma su himmatu wajen […]
daukacin Katsinawa sun san cewa Gwamna Ibrahim Shehu Shema ya bayar da muhimmiyar gudunmuwa wajen raya Jihar Katsina, a tsawon mulkinsa na shekara takwas, musamman in an yi la’akari da asibitoci da makarantun da ya raya. Don haka duk wanda zai gaji Shema a Jihar Katsina yana da matukar alfanu ga al’umma su himmatu wajen ganin ya dore da ayyukan raya kasa, don gina al’umma da muhallinsu.
Allah Ya albarkaci Jihar Katsina da hazikan mutane, wdanda suka shahara a fannmonin ilimi da ciniki da masana’antu da harkokin mulki, amma a ’yan shekarun nan ba a samu wanda ya yi rawar gani ba kamar Gwamna Shema, musamman in an yi la’akari da yadda ya kirkiro makarantar koyon sana’a, don kada matasanmu su ci gaba da zaman kashe wando. Sannan ya yi hidima wajen samar da takin zamani, don inganta harkokin noma, musamman ma saboda Bahushe ya ce, ‘da ruwan ciki a ke jan na rijiya.”
A fannin kula da lafiyar al’umma kuwa, Gwmana Shema ya gina asibitin kashi mallakar jiha, wanda a daukacin fadin Arewacin kasar nan babu irinsa. Ganin irin hobbasa da wnanan bawan Allah Ya yi wa al’umma, gas hi kuma zai sauka, har ta kai ga yana kokarin nada wani ya gaje shi, to wajibi ne ya tabbatar wa al’umma Jihar Katsina cewa, mutumin duk da zai gaje shi lallai zai dora a kan ayyukan da ya aiwatar a tsawon mulkinsa. Duk da cewa Musa Nashuni ya yi Kwamishina a gwmanatin Shema, kuma a iya cewa tare da shi aka aiwatar da ayyukan raya kasa, yana da kyau ya tabbatar wa al’umma cewa zai iya, kuma a shirye yake da ya dora a kan ginin maigidansa, ta yadda al’umma za su ce Alla sambarka.
Kowa ya san yadda ’yan siyasa ke yunkurin raba kuri’un al’umma a wannan zakara, har ta kai ga wasu na yi mana karyar za su raba mana zakara ko ma har da kaza ne. Wasu kuma sun ce za su yi abin da Gwamna Shema bai yi ba. To, mu dai ba ma son zakara, don ba neman suna muke so, aiki muke so a yi, ba aika-aika ba.
A halin gaskiya ba alkawuran ’yan siyasa suka dame mu ba, tunda kowa ya yi hankalin sanin mayaudari da wanda yake a kan doron gaskiya. In duk kajin kasar nan za ka yanke ka ba mu mu cinye, ai ba ka taimake mu ba, domin mun yi bikin dare daya ne kawai. Amma idan ka yi mana ayyukan raya kasa, mu mun san ‘ya’ya da jikokin al’ummar Katsina sai sun ci gajiyar wadannan ayyuka. Idan kuma ka ce za ka yi mana abin alherin da Shema bai yi ba, to ka nuna abin da ka aiwatar gwargwdon damar da ka samu a rayuwa.
A wannan gabar ina rokon Maigirma da ya shimfida mana hotunan makarantar koyon sana’a ta Katsina da Asibitin kashi da tallafin da aka bai wa mata a daukacin asibitocin gwmanati da ke fadin jiharmu, duk mu gansu a jaridar Aminiya da suaran jaridun Hausa, tunda da Hausa ake yi, kuma kai ne Sarkin Yakin Hausa a kasar Hausa. Kuma ka nuna mana yadda ake yi wa shanu allurar rigakafin huji da kare su daga sauran cututtuka, tunda kai ne sarkin Fulani. Lallai lokaci ya yi da za mu ga hotuna da bayanan wadannan ayyuka a Aminiya da sauran jaridun Hausa.
Idan har gwamna ya amsa wannan roko da na yi masa, to zai ba mu dama mu yi zaben nagari maida kudi gida, amma aikata sabanin haka zai sanya a yi zaben tumun dare. Don Allah Gwmna Shema tunda ka tabbata mai kaunar Katsinawa, kada ka bari a yi mana sakiyar da babu ruwa.
Idan Katsinawa suka smau wanda zai kwatanta ayyukan raya kasa da kyautata rayuwar al’umma kamar Gwmna Shema, to babu makawa kowa zai koyi kiwon zakara, har ya tara kaji da zakaru ba tare da wani ya lasa masa zuma a baki ba. Al’amari dai mafi a’ala, shi ne kiwon lafiya ba kiwon zakara ba.
A karshe dai, ina so al’ummar Jihar Katsina su gane cewa, muna bukatar gwamnan da zai kula da talakawa, ta yadda kowa zai ji cewa ana yi masa adalci. Wannan adalci kuwa zai tabbata ne a kowane fage na ruwa, tun daga kan ilimi da kiwon lafiya da hanyoyin ababen hawa da inganta noma da kiwo da samar da daukacin kayan more jin dadin rayuwa.
Mu dai ba ma kyamar kowa, manufar mu kawai a raya kasa, a kyautata rayuwar al’umma. Sannan masu mulki su sauke nauyin d aya rataya kansu, su kuma talakawa su bi doka da oda. Yin haka ne zai sanya al’umma ta zuana lafiya.
Mai girma Gwmana Shema muna zuba ido mu ga tallarka ta ayyukan raya kasa, tare da hotunan ayyukan raya kasa. Idan ka yi mana haka, ba sai ka tallata wani dan takara ba. Kai muna iya cewa ka koma gidan ka sha kuruminka. Domin Hausawa sun ce, ‘gani ya kori ji.’ Mu kuma Katsinawa Allah Ya sanya kada mu yi zaben tumun dare. Allah dai ya bai wa kasar nan shugabanni nagari, ya kuma tsareta daga bala’o’in da suka addabe mu. Amin.
Hassan Batuci Muhammadu ya rubuto makalarsa daga Abuja