Katu ta bayar da umarnin tsare sajan bogi a Ilorin
Kotun majistiri a Ilorin babban birnin jihar Kwara yau Alhamis ta umarci a tsare wani mai suna Alade Dayo a gidan yarin Oke-kura saboda laifin shiga aikin sojan Najeriya na bogi. Alkaliyar kotun Misis E. K Abu ce ta bayar da umarnin, saboda samun wanda ake tuhuma da laifuka hudu wanda suka hada da: yaudara […]
Kotun majistiri a Ilorin babban birnin jihar Kwara yau Alhamis ta umarci a tsare wani mai suna Alade Dayo a gidan yarin Oke-kura saboda laifin shiga aikin sojan Najeriya na bogi.
Alkaliyar kotun Misis E. K Abu ce ta bayar da umarnin, saboda samun wanda ake tuhuma da laifuka hudu wanda suka hada da: yaudara da damfara, cutar da jama’a da kuma razana jama’a.
Jami’in dan sanda Sajen Abideen Oderinde ne shigar da karar a kotun, daga hedkwatar ‘yan sandan unguwar Surulere a garin Ilorin.