kauna (2)

Mene ne kauna? Kalmar kauna tana da saukin fadi a baki; amma tana da wuyar fassara, yawancin lokaci idan muka ji irin bayanin da ke akwai kan wannan kalma mai saukin fadi, sai mu yi mamaki koda gaske ne mun san abin da muke fadi. Ina so mu ga yadda wannan kalma take bisa ga […]

kauna (2)
kauna (2)

Mene ne kauna?

Kalmar kauna tana da saukin fadi a baki; amma tana da wuyar fassara, yawancin lokaci idan muka ji irin bayanin da ke akwai kan wannan kalma mai saukin fadi, sai mu yi mamaki koda gaske ne mun san abin da muke fadi. Ina so mu ga yadda wannan kalma take bisa ga binciken masana; za mu yi nazari a kan wasu kalmomi cikin harshen Helinanci don mu samu gane irin kaunar da muke son kowane dayanmu ya samu.
Eros: Wannan soyayya ce da ke tsakanin namiji da mace; takan kai har ga yin jima’i. Irin wannan soyayya takan samu tsakanin miji da mata. Ita ce kuma takan kai ga yin zina, sai ka ji wani kato ya kwantar da muryarsa yana magana da wata budurwa ko yarinya, yana ce da ita masoyiyata; ‘rabin raina’ da maganganu iri-iri domin kawai ya jawo ra’ayinta, da zarar ya kwana da ita; shi ke nan. Sai mu lura domin ba ita ce kaunar da muke so mu yi magana a kai yau ba.
Philia/Philio: Wannan kuma soyayya ce irin wadda ake samu tsakanin iyali, tsakanin iyaye da ’ya’yansu, da kuma tsakanin abokai da dangi; har wa yau ba ita ce irin kaunar muke so mu yi magana a kai ba a yau.
Agape: Wannan ita ce nuna soyayya ga wani ko kuwa wata fiye da nuna kauna wa kanmu, masu magana sukan ce ‘so duka so ne, amma son kai ya fi,’ irin wannan soyayya ana yin ta ne ba domin komai ba, ba domin za mu samu wata riba ga kanmu ba, ba domin za mu samu tagomashi daga wurin wanda muke nuna wa wannan kauna ba, amma domin kawai mun ga ya yi kyau mu nuna irin wannan soyayya. Gaskiyar ita ce za mu iya nuna wannan kauna har ga wadanda muke gani su abokan gabanmu ne, babu wani abu da zai iya hana nuna irin wannan kauna ga kowane mutum a fuskar wannan duniya. Ba za mu iya bayyana irin wannan kauna a rayuwarmu ta yau da kullum ba, muddin ba mu da ruhun Allah zaune a cikinmu.
Maganar Allah na cewa “…..gama an baza kaunar Allah cikin zukatanmu ta wurin Ruhu Mai tsarki wanda aka bayas a gare mu.” (Rom.5:5). irin wannan kauna daga wurin Allah take ta wurin ikon Ruhunsa Mai tsarki. Wannan irin kaunar ce muke so mu yi nazari a kai.
A lokacin da Ubangijinmu Yesu Kiristi yake cikin wannan duniya; wadansu manyan malamai da marubuta sun je wurinsa da wata tambaya, suna cewa: “Wani daga cikin marubuta ya zo, ya ji su suna tambayar junansu, ya sani kuma Yesu ya amsa musu da kyau, ya tambaye shi, Wace doka ce ta fari cikin duka? Yesu ya amsa, Ta fari ke nan, ku ji, ya Isra’ila; Ubangiji Allahnmu, Ubangiji daya ne: kuma ka yi kaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da dukan azancinka da dukan karfinka. Ta biyu kuma, ka yi kaunar makwabcinka kamar ranka. Babu wata doka da ta fi wannan girma. Marubucin ya ce masa, Hakika, Malam, ka fadi daidai Shi daya ne; babu wani kuma sai Shi: kuma mutum ya kaunace Shi da dukan zuciya da dukan azanci da dukan karfi, ya yi kaunar makwabcinsa kuma kamar ransa, wannan ya fi gaban dukan baye-baye na konawa da hadayu nesa. Sa’anda Yesu ya gane ya amsa da hankali, ya ce masa, Ba ka da nisa da mulkin Allah ba, Bayan wannan ba wanda ya yi kuru da za ya tambaye shi kuma komai ba.” (Markus 12:28 – 34). Bisa ga koyarwar Yesu Kiristi Ubangijinmu, kaunar makwabci ya zama dole ne, makwabcin nan kuwa; ba lallai ba ne ya zama makwabcin kirki, mai hankali, ko ma yaya halin wannan makwabcin yake, akwai nauyin da Allah ne da kanSa Ya rataya a wuyan kowane mai bin Yesu Kiristi: wannan kuwa shi ne mu nuna kauna. kauna halin Allah ne da kanSa. Abu na biye shi ne; Allah Yana so mu kaunaci kowane makwabcinmu kamar ranmu, wannan ba da sauki yake ba ko kadan; musamman a wannan zamani da muka samu kanmu a ciki, yau cikin kasarmu, muna zaman ‘doya da manja’ kawai, tunanin da ke cikin zuciyar mutane sai Allah kadai Ya sani, amma bisa ga abin da kunne ke ji da abubuwan da baki ke fadi da irin halayen kiyayya da ake nunawa a fili, mun sani babu jituwa tsakanin jama’a; kowa na shakkar kowa. Idan har irin wannan tunani bai canja ba, to gaskiya babu yadda za mu samu zaman lafiyar da muke so mu gani cikin wannan kasa tamu; Masu bi dole ne mu shiga gaba cikin nuna wannan hanyar kauna idan da gaske ne muna nin Yesu Kiristi.
Yaya wannan kauna ke bayyanuwa?: Yaya mutum zai san ko yana dauke da irin wannan ruhu na kauna? “kauna tana da yawan hakuri, tana da nasiha, kauna ba ta jin kishi, kauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta bida wa kanta, ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura, ba ta yin murna cikin rashin yin adalci, amma tana murna da gaskiya, tana jurewa da abu duka, tana gaskanta abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka, kauna ba ta karewa dadai: amma koda zantattukan annabci, za a kawar da su; ko da harsuna, za su tuke; ko da ilimi, za a kawar da shi.” (1Kor.13:4 – 8).
Bari mu duba kalmomin da Littafi Mai tsarki ya ambata domin mu san abin da Allah ke nufi, mu kuma iya auna kanmu, mu gani ko muna da irin kaunar nan da Allah Yake so mu zama masu ita?
Hakuri:  Iya daure wa kowace wahala na tsawon lokaci, ba tare da bata rai ba.
Nasiha:  Son kyautata wa wadansu, kana marmarin ganin mutane suna murna, kana da kirki.
Ba ta jin kishi: Babu guna-guni cikin zuciya ko kuwa bakin ciki cikinka domin wani ya samu ci gaba. Babu kyashi cikin zuciya domin wani ya samu abin da kai ba ka da shi.
Ba ta fahariya: kauna ba ta yin burga, ba ta cika baki, ta nuna cewa ta isa.
Ba ta yin kumbura: kauna ba ta alfahari, ji da kai, kauna ba ta yabon kai.
Ba ta yin rashin hankali: kauna ba ta nuna rashin kunya, ba ta nuna rashin da’a, amma tana da ladabi.
Ba ta bida wa kanta: Irin wannan kauna ba ta son kai, amma tana tunanin kyautata wa makwabcinta.
Bi ta jin cakuna: Ba ta bata rai da mutane nan take; ba ta barin abu ya bata mata rai.
Ba ta yin nukura: Irin wannan kauna ba ta rike mutum a zuciya, ba ta rubuta laifin mutane; akwai saurin gafartawa.
Ba ta yin murna cikin rashin adalci: Tana murna ne kawai cikin gaskiya.
Tana jurewa da abu duka
Tana gaskanta abu duka
Tana kafa bege ga abu duka
Tana daurewa da abu duka..
Idan Allah Ya bar mu cikin masu rai makon gobe, za mu yi nazari a kan yadda za mu iya rayuwa kamar yadda Allah Yake so.