kauna (6)
Me kan sa kaunar Allah ta yi aiki?“Kamar yadda na bidi gare ka ka jinkirta zamanka cikin Afisus, sa’anda ina cikin tafiyata zuwa Makidoniya, domin ka dokaci wadansu mutane kada su yi koyarwa daban, kada kuwa su lura da tatsuniyoyi da lissafin asalai wadanda ba su da iyaka, wadanda sukan jawo muhawara, ba su aika […]
Me kan sa kaunar Allah ta yi aiki?
“Kamar yadda na bidi gare ka ka jinkirta zamanka cikin Afisus, sa’anda ina cikin tafiyata zuwa Makidoniya, domin ka dokaci wadansu mutane kada su yi koyarwa daban, kada kuwa su lura da tatsuniyoyi da lissafin asalai wadanda ba su da iyaka, wadanda sukan jawo muhawara, ba su aika wakilcin Allah wanda ke cikin ban-gaskiya ba, haka nan kuma ni ke yi yanzu. Amma matukar doka kauna ce mai fitowa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai nagarta da ban-gaskiya mara riya: wadansu kuwa cikin kuskure wadannan al’amura sun ratse zuwa cikin zancen banza; suna so su zama masu koyar da shari’a, koda shike ba su fahimci abin da suke fadi ba, ko baicin abin da su ke karfafa shaidarsu…”
Bari mu sake duba wannan wuri a sabuwar juyi “Kamar yadda na roke ka, ka dakata a Afisa sa’ad da za ni kasar Makidoniya, ka gargadi wadansu mutane kada su koyar da wata koyarwa daban, kada kuma su bata zarafinsu a wajen almara da yawan kididdigar asali marar iyaka, wadanda sukan haddasa gardandami, a maimakon rikon amanar al’amuran Allah da ban-gaskiya. Alhali kuwa manufar gargadinmu kauna ce wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kauna sahihiyar ban-gaskiya. Wadansu sun kauce wa wadannan al’amura, har sun baude, sun shiga zancen banza. Suna burin zama masana Attaura, ba tare da sanin abin da suke fada ba, balle matsalar da suke takamar hakikkicewa a kai.” (1Tim.1:3–7).
Daga inda muka yi karatu a sama, za mu ga abubuwa kashi uku da dole mu zama da su har idan muna son mu ga yadda kaunar Allah za ta bayyana Zuciya mai tsabta ko tsarkakakkiyar zuciya Lamiri mai nagarta ko lamiri mai kyau.
Ban-gaskiya mara riya ko sahihiyar ban-gaskiya.
Bari mu dube su daya-daya
Zuciya mai tsabta ko tsarkakakkiyar zuciya:
Yesu Kiristi ya yi magana a cikin Littafin Matta: 5:8 ya ce: “Masu albarka ne masu tsabtar zuciya gama za su ga Allah. Haka nan a cikin sura 12: 33-35, Yesu Kiristi ya sake cewa “Ko a maida itace mai kyau ’ya’yansa kuma masu kyau; ko kuwa a maida itace rubabbe, ’ya’yansa kuma rubabbu: gama bisa ga ’ya’ya ana sansance da itace. Ku haifaffun kasa, kaka za shi yiwu ku, da kuke miyagu, za ku zantar da abin kirki? Gama daga cikin yalwar zuciya baki yakan yi magana. Nagarin mutum daga cikin ajiyarsa mai kyau yakan fito da masu kyau: mugun mutum daga cikin mugunyar ajiyarsa yakan fito da miyagu.” Zuciyar mutum abu ne da sai an bi ta a hankali, domin za ka iya tsayuwa da wani wanda idan da so samu ne, zai so ya wulakanta ka ko ma ya kashe ka idan da zai yiwu, amma kuma ba za ka karanta a fuskar mutumin ba; domin yana cikin zuciyarsa ne.
A cikin nazarin da muka yi wanda ya gabata, mun ga cewa Allah da kanSa kauna ne, to idan har muna so mu ga cewa Ubangiji Allah Ya ba mu daga cikin ainihin irin kaunar da shi da kanSa yake, ya zama dole ne mu zama da tsabtar rai. Zuciya mai tsabta ko tsarkakakkiyar zuciya; zuciya ce da ta bar Ubangiji Allah ya yi aikinsa a kanta, zuciya ce mai tsarki da ba ta tunanin mugunta game da wani kuma akwai tsoron Allah a ciki: haka nan za mu iya sanin mai tsoron Allah ta wurin yin biyayyarsa ga maganar Allah ko umarninSa. Mutum mai tsabtar zuciya, yakan iya gafarta wa wadanda suka yi masa laifi ya kuma iya kaunarsu. Tsarkin zuciya ta kan sauya rayuwarmu ga nuna diyar Ruhu a cikin rayuwar mu ta yau da kullum kamar yadda muka gani a cikin Littafin Galatiyawa: 5:22–26. “Amma diyan Ruhu kauna ne, farin ciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa, irin wadannan babu shari’a a kansu. Su kuma wadanda suke na Kiristi Yesu sun giciye jiki tare da gurinsa da sha’awoyinsa. Idan muna rayuwa bisa ga Ruhu, bisa ga Ruhu kuma mu yi tafiya. Kada mu zama masu homa, muna cakuna juna, muna yi wa juna hassada.”
Allah da kanSa ne Yake tsarkake zuciyar mutum, shi ya sa dole ne mu samu zuwa wurinsa a kullum dominYa tsarkake zuciyarmu wurin jinin Yesu Kiristi.
Lamiri mai nagarta ko lamiri mai kyau:
Lamiri dai mazaunin tunani ne a cikin mutum da kan sa mu iya sanin abin da ya dace da abin da bai dace ba. Wuri ne a cikin mutum da za ka iya shar’anta kanka game da sanin abin da ke daidai da abin da ba daidai ba. Idan har muna so mu ga irin wannan kaunar ta bayyana, dole lamirinmu ya zama da salama. Muddin cikin lamirin mutum ba salama, babu yadda zai iya tunani mai kyau. Lamirin mutum na nan kamar wata kararrawa ce ta Allah; idan ta tashi, sai ta jawo hankalin mutumin ga dangantakarsa da Allah. Manzo Bulus, ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki ya ce a cikin Littafin Ayyukan Manzanni: 24:16 cewa “Saboda haka, a kullum nake himma in kasance da lamiri marar abin zargi a wurin Allah da wurin mutane.” Muna bukatar mu zama da irin wannan kyakkyawan lamiri domin mu iya zuwa gaban Allah gaba-gadi ba tare da wani tsoro ba, musamman ma lokacin da muna zuwa gabanSa cikin addu’a. Hakan nan ne za mu karbi irin wannan kaunarsa mu kuma iya nuna ta ga wadansu da suke kewaye da mu.
Ban-gaskiya mara riya, ko sahihiyar ban-gaskiya:
Rayuwar kowane mai bin Yesu Kiristi rayuwa ce ta ban-gaskiya. Babu yadda mai bi zai ci nasara cikin komai in ba ta wurin ban-gaskiya ba. A kashin gaskiya maganar Allah ta ce babu ma yadda mutum zai gamshi Allah idan ba tare da ban-gaskiya ba. A cikin Littafin Ibraniyawa: 11: 6; maganar Allah ta koya mana cewa: “Ba shi yiwuwa a gamshe Shi, sai tare da ban-gaskiya: gama mai zuwa wurin Allah sai shi ba da gaskiya akwai Shi, kuma Shi mai sakawa ne ga wadanda suke bidarSa.” Haka nan a cikin Littafin 1Yohanna 3: 23 – Maganar Allah na cewa: “Umarninsa ke nan, mu ba da gaskiya ga sunan dansa Yesu Kiristi, mu yi kaunar junanmu kuma, kamar yadda ya umurce mu.” Hanyar ban-gaskiya ita ce hanyar kawai, babu wata hanya da za mu iya bi domin mu gamshi Ubangiji Allah sai ta hanyar ban-gaskiya kadai. Dole mu yarda da shirin Allah game da tsare rayuwarmu. Abin nufi shi ne; mu yarda mu mika ragamar mulkin rayuwar ga Allah, haka nan kuma za mu ga bayyanuwar kaunarSa cikin rayuwarmu. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.