kauna ta sa mutum ya shafe shekara shida yana tara hoton Sarkin Dubai

  Filipe D’melo mai shekara 67 ya shafe shekara shida yana tara hotunan Sarkin Dubai, Firayiministan Hadaddiyar Daular Llarabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum. Cikin shekara shida, wannan mutum mai kaunar sarki ya tara hotuna sama da dubu hudu na Sheikh Mohammed. Hotunan Sarkin dubai sun baibaye bangon gidansa, baya ga wadanda ya yi […]

kauna ta sa mutum ya shafe shekara shida yana tara hoton Sarkin Dubai

 

Filipe D’melo mai shekara 67 ya shafe shekara shida yana tara hotunan Sarkin Dubai, Firayiministan Hadaddiyar Daular Llarabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum.

Cikin shekara shida, wannan mutum mai kaunar sarki ya tara hotuna sama da dubu hudu na Sheikh Mohammed. Hotunan Sarkin dubai sun baibaye bangon gidansa, baya ga wadanda ya yi musu kundi da jera su kamar riguna a gidansa da ke  Meena Bazar. Sannan wasu hotunan da suka kai kimanin 500 da ba su samu wuri a gidansa ba, ya kai su gidansa na Goa.

Bayan wannan al’ada ta tara hotunan, har wakokin yabo ya yi wa Sarkin Dubai.

D’melo mutum ne da ya shafe sama da shekara 40 a Hadaddiyar Daular Larabawa, inda a halin yanzu yake shirin komawa kasarsa Indiya nan da shekara ta 2019. Sai dai yana da buri guda da yake fatan cikarsa, warto ya gana da Sarkin Dubai Sheeikh Muhammad, don ya mika masa kyautar kundin hotuna 375 da ya yi masa.

Ya ce matukar bai samu ganawa da sarkin ba, al’amarin zai dade yana sosa zucciyarsa.

Lokacin da D’melo ke bayani kan wannan burin nasa, sai ya idanunsa suka cika da kwalla, inda yake rokon ganin ya hadu da Sarkin Dubai. ‘Idan wani ya taimaka mini na gana da Sheikh Mohammmeed, a shirye nike a kodayaushe in je in yi masa sallama “Assalaam Walaykum” lokacin da zan koma gifda. Ina zubar da hawayen jin dadi saboda bayyana abin da ke cikin zuciyata,” inji shi.

Duk da cewa har uanzu bi kai ga gaci ba, D’melo ya ce ba zai gajiya ba. “Idan har Ubangiji zai cika mini buri guda, to ya ba ni damar haduwa da Sheikh Mohammed, kuma ina da tabbbacin cewa wata ran azan gana da shi kafin in bar kasar nan.