‘Kaunar Buhari ta kawo mana hadin kai a Kudu’
A yayin da lokacin zaben 2019 ke kara gabatowa, lamarin da ya sanya masu neman madafun iko da masu mara musu baya ke kara yin azama don ganin sun samu goyon bayan jama’a da samum kuri’unsu, a Jihar Legas da sauran jihohin Kudu maso Yamma, al’ammar Arewa mazauna yankin sun bayyana samun wanzuwar hadin kai a […]
A yayin da lokacin zaben 2019 ke kara gabatowa, lamarin da ya sanya masu neman madafun iko da masu mara musu baya ke kara yin azama don ganin sun samu goyon bayan jama’a da samum kuri’unsu, a Jihar Legas da sauran jihohin Kudu maso Yamma, al’ammar Arewa mazauna yankin sun bayyana samun wanzuwar hadin kai a tsakaninsu sakamakon soyayyarsu ga Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, inda suka ce hakan ya dinke baraka da bambance-bambancen dake tsakaninsu.
’Yan Arewar sun bayyan haka ne a wani taron hadaka da suka yi a garin Agege wanda ya samu wakilcin shugabanni uku-uku daga kowace jiha ta Kudu maso Yamma a karkashin kungiyar hadaka da ke mara wa kudirin sake zaben Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo wacce Alhaji Shafi’u Sulaiman Tofa ke yi wa jagoranci.
Taron ya mai da hankali ne kan muhimmancin shigar ’yan Arewa mazauna Kudu al’amuran siyasa, inda suka ce hakan ne kadai zai ba su cikaken ’yanci tare da kwarin gwiwar gudanar da al’amuransu na yau da kullum kamar yadda sauran kabilun yankin ke yi.
Shugaban Kungiyar Hadakar, Alhaji Shafi’u Sulaiman Tofa ya shaida wa Aminiya cewa a baya ’yan Arewa mazauna Kudu sun yi sakaci, amma a yanzu sun farka daga barci, ya ce soyayyarsu ga Shugaba Buhari ce musababbin farkawarsu domin ta zamo inuwa guda da kan hada kan ’yan Arewa mazauna yankin, abin da a baya ba haka lamarin yake ba.
Ya ce za su yi amfani da wannan dama wajen ziyartar sarakunan gargajiyar a yankin tare da neman goyon bayansu wajen dinke baraka da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, “Wannan tafiya tamu ba ta tsaya ga siyasa kadai ba, abu ne da ya shafi al’amuran rayuwarmu baki daya, don haka za mu yi amfani da wannan dama ta hanyar kara dankon zumunci tare da dinke baraka. Mu da ke zaune a nan Kurmi mun san amfanin da jagorancin Shugaba Buhari ya kawo mana, a baya ba mu da kima, an dauke mu cima-zaune ko ’yan ta’adda, amma tun lokacin da Shugaba Buhari ya dare karagar mulki muka samu kima da mutunci ta yadda yanzu in an ga Bahaushe ana daukarsa cikakken mutum,” inji shi.
Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu daya ne daga cikin shugabanin ’yan Arewa mazauna Legas kuma mai yin fashin baki kan al’amuran yau da kullum, ya halarci taron hadakar, ya kuma shaida wa Aminiya cewa Buhari da Osibanjo su ne zabin ’yan Arewa mazauna jihohin Kudu maso Yamma, domin sun lura da alfanun haka.
Ya ce “Kuma dama jihohin Yarbawa Buhari da Osinbajo ne zabinsu, kuma mu da muke zaune a wadannan jihohin muna nan rike da shawarar da Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello ya ba mu, inda ya ce kada mu sake mu saba wa tsarin siyasar jihohin da muke a zaune. To ka ga in mun rike wannan shawara a koyaushe tsarin siyasarmu za ta zamo daidai da ta wannan yanki, to ka ga ai ba mu da ja ke nan, domin faduwa ce ta zo daidai da zama.”
Mahalarta taron sun sha alwashin wayar wa junansu kai a kan muhimmancin karbar katin zabe na dindindin tare da zaben shugabanin da tsarinsu da nagartarsu za ta amfanar da al’umma.