kaunar da ke tsakanin Shata da mijina ne ta sa ya yi mini waka- Aishatu ’Yanleman

Hajiya A’ishatu ’Yanleman tana daya daga cikin wadanda marigayi Dokta Mamman Shata Katsina  ya yi wa waka. Aminiya ta tattauna da ita a gidansu da ke unguwar Ebute-Meta a Jihar Legas, inda ta bayyana dalilan da suka sa ya yi hakan da kuma sauran batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance: Ranar Haji Ai ’Yanleman,Ni ’Yanleman […]

kaunar da ke tsakanin Shata da mijina ne ta sa ya yi mini waka- Aishatu ’Yanleman

Hajiya Aishatu ‘YanlemanHajiya A’ishatu ’Yanleman tana daya daga cikin wadanda marigayi Dokta Mamman Shata Katsina  ya yi wa waka. Aminiya ta tattauna da ita a gidansu da ke unguwar Ebute-Meta a Jihar Legas, inda ta bayyana dalilan da suka sa ya yi hakan da kuma sauran batutuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Ranar Haji Ai ’Yanleman,
Ni ’Yanleman na ka koma- Ranar Haji Ai ’Yanleman
Mu je yawo mu kwana biyu- Ranar Haji Ai ’Yanleman
Mu je wurin waliyan Allah mu gaggaisa-Ranar Haji Ai ’Yanleman
’Yanleman na ka koma-Ranar Haji Ai ’yanleman.

Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinki?
Hajiya Aishatu: Sunana Hajiya Aishatu Amadu, sunan mijina Alhaji Widi dan Tijjani wanda Shata ya yi wa waka. Mu asalinmu mutanen garin ’Yanleman ne da ke Jihar Jigawa. Mu Fulani ne na asali, amma muna jin Hausa sosai da sosai. Mun dade a Jihar Legas, kusan in ce mun zama ’yan kasa a nan jihar. Domin gaskiya mun yi shekaru da yawa a Legas.
Aminiya: Bayan mijinki, Ke ma Shatan ya yi miki waka?
Hajiya Aishatu: kwarai kuwa Alhaji Mamman Shata ya yi mini waka mai suna Ranar Haji Ai ’Yanleman. Wakar ta shiga duniya kuma ta samu karbuwa a wurin jama’a. Ta yi suna sosai kuma mutane sun san ta saboda gidajen rediyo na ciki da wajen Najeriya suna sanya wakar. Gaskiya wakar ta tsaru sosai saboda Shata ya nuna bajinta da kwarewa. Alhaji Mamman Shata ya wasa ni sosai a wakar kuma wakar ta yi dadi kwarai da gaske.
Aminiya: Me ya sa kike jin Shata ya yi miki waka?
Hajiya Aishatu: Soyayya ce tsagwaronta da ke tsakaninsa da maigidana (Alhaji Widi) ya sa Shata ya yi mini wakar. Domin a lokacin da Shata zai wakar bai sanar da mu ba sai kawai jin faifan wakar muka yi a gari mutane suna sauraro. Shata bai gaya mini cewa zai yi mini waka ba. Kuma wallahi babu abin da na bashi na kyauta. Shi Shata wani irin mutum ne, Kudi ba su sanyawa ya yi maka waka sai ya ga dama. Saboda haka ni bai taba sanar da ni cewa zai yi mini waka ba. Kuma bai taba yi mini alkawari cewa zai yi mini waka ba. Tun a wannan lokacin na yarda cewa Shata sai ya ga dama yake yi wa mutum waka. Kuma yana waka ne ba saboda abin duniya ba.
Aminiya: Bayan Shata akwai wani mawakin da ya taba yi miki waka?
Hajiya Aishatu: Banda Shata akwai mawakain da ya yi mini waka. Mawakin kuwa shi ne dan Maraya Jos. Amma ita na manta yadda take. Shi ma ya zo har nan gidan ya yi wasa kuma wasan ya kayatar sosai.
Aminiya: A lokacin da Shata ya yi miki waka ya kai shekara nawa?
Hajiya Aishatu: Gaskiya shekarun da yawa domin ya kai shekara kusan 50. Kuma a wannan lokacin kusan kowane gidan rediyo yana sanya wakar a kai a kai. Kuma duk lokacin da aka sanya wakar a rediyo ina jin dadinta kuma takan sanya na tuna baya.
Aminiya: A lokacin da kika ji wakar da Shata ya yi miki yaya kika ji a ranki?
Hajiya Aishatu: Gaskiya na ji dadi sosai domin sunana ya shiga duniya. Ai a wancan lokaci idan Shata ya yi maka waka ai abin alfahari ne. Domin mutane za su san sunanka ko’ina, ko wane sako da lungu za a ji sunanka. Saboda haka ba karamin abin alfahari ba ne. Kuma ba karamar daukaka ba ce.
Aminiya: Akwai alaka da take tsakaninku da iyalan Shata?
Hajiya Aishatu: Gaskiya babu wata alaka tsakaninmu da iyalan Shata sai da ya mutu ma muka san dansa da ke yin waka a yanzu. Babu alaka ta auratayya ko ta wani abu sai dai alaka ta shi masoyin maigidana ne.Allah ya hada jininsu. Shi maigidanmu yana kaunar Shata, shi ma Shata yana kaunarsa.

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato