Kaunar da mijina ya ke min ta wuce gona da iri, a raba aurenmu
Mun samu wani rahoto mai cike da ban mamaki na wata matar aure Musulma da ta nemi a raba ta da mijinta saboda kawai babu abin da ya sani a cewarta sai zaman lafiya da yake da ita. A wani yanayi mai kama da almara, matar auren tana bukatar mijin ya sake ta don kawai […]
Mun samu wani rahoto mai cike da ban mamaki na wata matar aure Musulma da ta nemi a raba ta da mijinta saboda kawai babu abin da ya sani a cewarta sai zaman lafiya da yake da ita.
A wani yanayi mai kama da almara, matar auren tana bukatar mijin ya sake ta don kawai wata sa’insa ba ta taba shiga tsakaninsu ba.
Matar ’yar kasar Indiya ta garzaya wata kotun shari’a inda ta nemi a alkali ya warware igiyar aurenta da mijin nata, watanni goma sha takwas kacal bayan aurensu.
Jaridun kasar sun ce catar ta yi ikirarin cewa tsawagaron so da kauna da mijin ya ke nuna mata ta sha mata kai.
Ta shaida wa kotun cewa: “Ba ya taba kyara ta, kuma bai taba bata min rai ba. Wani lokacin har girki yake yi kuma ya taimaka min yin aikace-aikacen gida.”
“A duk lokacin da na yi kuskure ko na aikata ba daidai ba, sai kawai ya kawar da kai ya mai da komai ba komai ba ya nuna yafiyarsa a kan hakan. Ba ya tanka ni idan na nemi mu yi jayayya da shi.”
“Bana son irin wannan rayuwar da za a ce komai na yi daidai ne a wurin mijina”, inji matar.
Sai dai alkalin kotun ya yi watsi da bukatar sakin, lamarin da ya sanya ta mika bukatar zuwa ga wata majalisar dattawan kauye inda a nan ma hakarta ba ta cimma ruwa ba.
Daga bangaren mijin, ya ce yana matukar kaunar matarsa kuma yana son a koda yaushe ya faranta mata. Ya kuma bukaci kotun ta yi watsi da karar da matar tasa ta shigar.
Yanzu haka dai kotun ta nemi ma’auratan su sansanta kansu.