Kaurace wa shimfidar kwanciya ta sa za a raba auren shekara 20 a Kaduna
A ranar Laraba ne wata matar aure ta nemi wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Magajin Garin a Jihar Kaduna da ta katse igiyar aurenta da mijinta da suka kwashe shekaru 20 sun tare. Matar ta nemi kotun ta raba auren da ke tsakaninta ta mijinta domin a cewarta ko shimfida ta kwanciya […]
A ranar Laraba ne wata matar aure ta nemi wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Magajin Garin a Jihar Kaduna da ta katse igiyar aurenta da mijinta da suka kwashe shekaru 20 sun tare.
Matar ta nemi kotun ta raba auren da ke tsakaninta ta mijinta domin a cewarta ko shimfida ta kwanciya ba ta hada ta da shi.
- An fara bincike kan mutum biyu da suka mutu bayan karbar rigakafin Coronavirus
- Dillalan Shanu da kayan abinci za su janye yajin aiki
- An kashe dan kasuwa bayan biyan fansar N5m a Sakkwato
Matar wadda ke zaune a layin Kontagora cikin kwaryar birnin Kaduna, ta shaida wa Kotun cewa mijinta ya kaurace wa saduwar aure da ita na tsawon kimanin shekaru 11.
“Ba ya bani kulawar da ta dace da ni, ko da ina rashin lafiya kuwa don haka a yanzu na gaji gaskiya so nake kawai ya sawwake min,”a cewarta.
A nasa bangaren, mijin nata ya ce yayi iya bakin kokarinsa kan auren nasu amma yanzu haka shi ma bashi da sha’awar ci gaba da zama da ita.
Alkalin Kotun, Mai shari’a Malam Murtala Nasir, ya dage zaman sauraren karar zuwa 10, ga watan Maris don ci gaba da sauraron karar, inda ya bukaci kowannensu ya zo da waliyyinsa a zaman kotun nag aba.