kauyukan Shinkafi na cikin mawuyacin hali
Assalamu alaikum. Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga ma’aikatan Aminiya kwata! Bayan haka ina son ku ba ni dama domin in ce wani abu akan talakawan yankin kauyukan Shinkafi a nan Jihar Zamfara, zuwa yanzu talakawan yankin suna cikin wani mawuyacin hali Akwai rashin tabbas a kan fargabar kai musuhare-hare da dauki dai-dai da ake […]
Assalamu alaikum. Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga ma’aikatan Aminiya kwata! Bayan haka ina son ku ba ni dama domin in ce wani abu akan talakawan yankin kauyukan Shinkafi a nan Jihar Zamfara, zuwa yanzu talakawan yankin suna cikin wani mawuyacin hali Akwai rashin tabbas a kan fargabar kai musuhare-hare da dauki dai-dai da ake yi musu a yankin.
Ko shakka babu yanzu lokaci ne da ya kamata a ce a tura isasun jami’an tsaro a yankin domin akasarin mutanen yankin manoma ne, haka shi zai ba su damar sakin jikinsu domin ci gaba da gudanar da aikin gona al’amarin da ke gudana a yanzu.
Lallai al’umma ta hada karfinta wajen tainmakekeniya don shawo kan wannan al’amari da ya ki ci, ya kki ccinye.
Sannan mu kara da addu’o’I ko Allah ya klawo mana karshenj wannan matsala ta kasha-kasheen mutane da asarar dukiya. Kuma duk mai kishin Jihar Zamfara da ma kasar nan baki daya ya kamata mu yi tunanin mafita, tare da aiki a aikace wajen tunkarar irin wadannan matsaloli, ta yadda kafin mahukunta su kawo mana dauki mun san irin abin da za mu fara yi.
Bayan haka. Muna amfani da wannan damar domin kira ga mai girma Gwamnan jihar Zamfara kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (Hon, Dr, Abdul-azizu yari Abubakar shattiman zamfara) daya taimakawa iyalai da ‘yan uwan bayin Allan da wannan lamari ya rutsa dasu, daga karshe muna addu’ar samun zaman Lafiya a jihar Zamfara da Yankin Arewa dama kasa baki dai. Wassalam
Gusau/08133376020nura Muhammad Gusau <[email protected]>