Kawunan ‘yan majalisar Birtaniya sun rabu kan IS

An samu rabuwar kawuna a tsakanin ‘yan majalisar dokokin Birtaniya kan yunkurin da kasar ke yi na shiga kawancen sojin da Amurka ke jagoranta a yaki da kungiyar IS a kasar Siriya.Firaministan kasar, Dabid Cameron, ya ce IS na yin barazana ga tsaron Birtaniya, yana mai cewa mayakansu na yi wa mata fyae da kashe […]

Kawunan ‘yan majalisar Birtaniya sun rabu kan IS
Kawunan ‘yan majalisar Birtaniya sun rabu kan IS

An samu rabuwar kawuna a tsakanin ‘yan majalisar dokokin Birtaniya kan yunkurin da kasar ke yi na shiga kawancen sojin da Amurka ke jagoranta a yaki da kungiyar IS a kasar Siriya.
Firaministan kasar, Dabid Cameron, ya ce IS na yin barazana ga tsaron Birtaniya, yana mai cewa mayakansu na yi wa mata fyae da kashe Musulmi, “kuma dabbobi ne”.
Sai dai shugaban jam’iyyar hamayya ta Labour Party, Jeremy Corbyn, yana adawa da shigar Birtaniya cikin kawancen, yana mai cewa sojin kasar za su rika kashe fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba.
A cewarsa, miliyoyin ‘yan Siriya na son a sasanta domin kawo karshen yakin basasar kasar.
Kuma akwai dubban masu zanga-zangar da suke ci gaba da zanga-zangar a titunan birnin Landan, inda suke adawa da yunkurin da kasar ke yi na shiga kawancen sojin.
A shekarar 2013 ne ’yan majalisar suka ki amincewa da bukatar Mista Cameron game da kai wa Siriya hari.