Kayan amfanin gona sun cika kasuwannin Jihar Katsina 

Batun gyaran gidaje, harkokin aure da bikin Kirsimati sun janyo yawaitar kayan amfanin gona a kasuwannin Jihar Katsina a daidai wannan lokaci, yanayin da ya kawo wadatar masara da wake a makon jiya. Kamar yadda aka sani, a daminar da ta gabata wadansu daga cikin manoma sun yi asarar wasu sassa na gidajensu ko kuma […]

Kayan amfanin gona sun cika kasuwannin Jihar Katsina 

Sashin sayar da wake a Kasuwar Funtuwa

Batun gyaran gidaje, harkokin aure da bikin Kirsimati sun janyo yawaitar kayan amfanin gona a kasuwannin Jihar Katsina a daidai wannan lokaci, yanayin da ya kawo wadatar masara da wake a makon jiya.

Kamar yadda aka sani, a daminar da ta gabata wadansu daga cikin manoma sun yi asarar wasu sassa na gidajensu ko kuma gidajen baki daya sanadiyar ambaliyar ruwa da aka samu a wasu sassa. Hakan ya sa manoman fito da amfanin gonar da suka noma don sayarwa su gyara gidajen da suka lalacen. Wani manomi mai suna Umar Aminu daga Karamar Hukumar Kanƙara ya ce, baya ga batun gini ko gyaran muhalli, har ila yau, tsohuwar al’ada ce a duk karshen shekara jama’a su yi aure ga ’ya’yansu saboda sun samu abin da za su yi hidimar bikin daga sayar da amfanin gonar.

“Da kaka ne manomi yake samun sukunin warware wasu matsalolin da ya fuskanta a baya. Batun aure da gyaran gidajen da suka lalace sakamakon ruwan saman da ya shude na daga cikin dalilin da suke sa manomi ya kai amfanin gonarsa kasuwa don sayarwa wanda hakan yake kawo yawaitar kayan gonar a kasuwanni, kuma a samu saukar farashin kayan. Malam Umar ya ci gaba da cewa, manoma a bana sun noma masara da shinkafa da wake fiye sosai. Ya ce, bikin Kirsimeti na daga cikin dalilan da suka sa Kiristoci manoma fitar da abin da suka noma zuwa kasuwa domin samun abin yin shagulgulan bikin.

An ga ’yan kasuwa na ta hada-hadar sayen kayan abincin irinsu shinkafa da wake da tumatir da sauransu domin kaiwa Kudu, musamman garuruwa  Anaca daWarri da Fatakwal da Legas da Ibadan da sauransu.

Binciken Aminiya a kasuwannin Bakori da Funtuwa da Kafur da Sheme, ya gano cewa yawaitar amfanin gonar ya shafi farashin kayan. Bukatar shinkafar tuwo ’yar gida ya sa farashinta ya tashi daga Naira dubu 24 zuwa dubu 27 a kowane buhu mai nauyin kilo 100. Shi kuwa babban kwandon tumatir farashinsa ya tashi zuwa Naira dubu shida, maimakon dubu hudu a baya, buhun masara kuwa farashinsu ya sauko daga Naira dubu takwas zuwa dubu bakwai da dari biyar. Kazalika, farashin buhun wake ya rika sauyawa a tsakanin Naira 17,500 zuwa Naira 18,500 bisa kyan da ya fito da shi sabanin Naira dubu 20 da aka sayar da shi a mako uku da suka shude.

Malam Ibrahim Adamu daya daga cikin dillalan kayan amfanin gonar a Kasuwar Funtuwa ya ce, suna amfani da irin wannan lokacin domin sayen dawa da wake suna ajiyewa. “Saboda yawan bukatar da ake yi wa waken wanda kuma yakan dauki tsawon watanni bai lalace ba ya sa muke sayensa a yanzu mu ajiye har lokacin da zai fara karanci. Haka nan, dawa ma na daga cikin kayan amfanin gonar da wasu masana’antu ke bukata, shi ya sa ita ma muke saye muna ajiyewa. Sannan ga shi bana ba a noma ta sosai ba kamar bara,” inji shi.

Dan kasuwar ya kara da cewa, irin yadda ake kawo masara da yawa a kasuwar ya sa farashinta ya rika yin kwan-gaba-kwan-baya, wato a tsakanin Naira 7,500 zuwa Naira 8000.