Kayan da ake yi a kasar nan ya wuce na waje inganci – Iya Mashal Sadik
Babban Hafsan mayakan sama na Najeriya Iya Mashal Sadik Abubakar ya ce babu wani kayan da ake yi a kasar nan wanda bai wuce na kasashen waje inganci ba, Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Kamfanin Tamfol (Zaria Industry Limited- ZIL) da ke Dakace a Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna domin ganin […]
Babban Hafsan mayakan sama na Najeriya Iya Mashal Sadik Abubakar ya ce babu wani kayan da ake yi a kasar nan wanda bai wuce na kasashen waje inganci ba,
Ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Kamfanin Tamfol (Zaria Industry Limited- ZIL) da ke Dakace a Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna domin ganin yadda suke gudanar da ayyukansu tare da ganin irin kayayyakin da suke yi da za su yi dai dai da bukatun mayakan sama.
Iya Mashal Sadik Abubakar ya ci gaba da cewa bisa abin da idonsa ya gani a kamfanin, ya amince da sayen kayayyakin kamfanin domin amfanin cibiyoyinsu da makarantun mayakan saman Najeriya.
Shugaban mayakan saman ya ce bisa umarnin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar na yin amfani da kayan da ake samarwa a gida ne ya zaburar da shi domin daukar wannan mataki.
Ya ce, sauran masu sanye da kayan sarki su ziyarci Kamfanin ZIL domin gane wa idonsu kayayyakin da suke yi wadanda za su bukata ba sai an je wata kasa don sayowa ba.
Babban Hafsan ya nuna takaici kan yadda aka bar masana’antar ta durkushe alhali duk fadin Afirka ta Yamma babu kamarta.
Saboda haka ya tabbatar wa mahukunta kamfanin na hada hannu da su ta hanyar sayen kayayyakin da suke yi.
Da yake jawabi Shugaban Kamfanin Zaria Industry Limited, Injiniya Iliyas Saleh ya ce, a duk Nahiyar Afirka irin kamfaninsu guda hudu ne amma yanzu uku suka rage na Afirka ta Kudu da ta Masar sai Najeriya cikon ta hudu wadda ke kasar Libiya an rufe ta sanadiyyar rikicin da kasar ke ciki.
Injiniya Saleh ya bayyana jin dadinsa bisa ziyarar da Babban Hafsan Mayakan Saman Najeriya ya kai musu don ganin abubuwan da suke yi.