Kayan da’a: Mata a rika yi wa kai kiyamul– laili (3)
(5) Hana daukar Ciki: Wani lokacin kayan da’a sna hana daukar cikin ma kwata-kwata, misali, irin su Yashin Madina ta hanyar lalata mahaifa da su ke yi. Hakazalika sukan zauna a kokunan nan biyu masu samar da kwayaye (Obaries), da kuma kwaroro (Fallopian Tube or Obiduct) da ke da hakkin zuwa da komayyar kwayayen haihuwa, […]
(5) Hana daukar Ciki:
Wani lokacin kayan da’a sna hana daukar cikin ma kwata-kwata, misali, irin su Yashin Madina ta hanyar lalata mahaifa da su ke yi. Hakazalika sukan zauna a kokunan nan biyu masu samar da kwayaye (Obaries), da kuma kwaroro (Fallopian Tube or Obiduct) da ke da hakkin zuwa da komayyar kwayayen haihuwa, wanda a nan ne kuma cakuduwa (Fertilization) tsakanin kwkyayen da maniyyin namiji da kwayayen haihuwa ke faruwa, inda sinadaran kayan da’a kan je su yi zaman dirshan a kwaroron, kasancewar sinadaran a wurin sai ya zamanto sun rage karfin kwayayen haihuwa da kuma maniyyin namiji, wanda a karshe dai ciki ya ki shiga.
(6) Cutar Kansa: Sakamakon amfani da kayan da’a na kawo cutar kansa (sankara) ta mahaifa. Wanda nan ma yake hana daukar ciki da kuma lalacewar mahaifa, wani lokaci kuma bayar da matsala wajen haihuwa, ko kuma a haifi yaron babu rai. Kana sakamakon amfani da kayan da’a yakan haifar da sankarar mama.
(7) Cutar Hawan Jini: Sakamakon amfani da kayan da’a na sha na haifar da hawan jini, kasancewar jini wani ruwa ne da ke tafiyar da abinci, ruwan da muka sha, da magungunan da muka sha, don haka kasancewar kayan da’a na dauke da wasu sinadarai masu lahani ga shi jinin, idan kuma aka yawaita amfani da kayan da’a (na sha), sai hakan ya kawo hauhawar jini. karshe dai a kamu da hawan jini.
(8) Matsanancin Ciwon Kai: Kayan da’a na janyo matsanancin ciwon kai, da kuma dumamar ko zafin jiki. Kamar yadda wasu matan da aka kwantar da su sakamakon amfani da kayan da’a su ka shaida mini, inda su ka sanar da ni, “bayan wani ruwa da yake zuba daga al’aurasu, kuma lokaci zuwa lokaci sukan ji matsanancin ciwon kai da kuma zafin jiki”.
(9) Ciwon Zuciya: Amfani da kayan da’a na haifar da ciwon zuciya, kasancewar magungunan kayan da’a da matan kan sha yana samun damar zaga jikinsu ne, ta hanyar zagaya sassan jiki da jini ke yi. Kuma da ma zuciya ita ta ke da hakkin harba jini izuwa kowane sashi na jikin dan Adam, sannan bayan jini ya gama zagaye jikin, yakan dawo zuwa zuciya. Kamar yadda na yi bayani a sama, cewa kayan da’a na kunshe da sinadarai da suke da lahani ga jini, don haka idan bayan jini ya kwashi wadannan sinadarai, ya zaga jiki da su, sannan ya dawo zuwa zuciya, hakan sai ta sanya taruwar wadannan sinadarai a zuciya, inda a nan sai ka samu sun haifar da ciwon zuciya, imma a samu kumburar fatar da take bada kariya ga zuciya wato, Pericadium, ko kuma haifar da nakasu ga ita zuciyar wajen harba jini zuwa ga sassan jiki, da dai sauran cututtuka.
(10) Ciwon Hanta: Amfani da kayan da’a na kawo ciwon hanta. Kamar yadda bayani ya gudana, wadannan kayan da’a su na dauke da sinadarai masu lahani ga garkuwar dan Adam. Jikin mutum ya na dauke da wasu gidaje da suke da hakkin tace abin da ke shige da fice da kuma zuwa da komayya a cikin jikin dan Adam.
A cikin wadannan gidaje akwai hanta, wacce ita take da hakkin bincike wajen tantance sinadaran da jini ya kunsha, don haka idan akwai sinadaran da suka yi wa gangar jiki lahani, sai ta tace shi, don haka idan suka yi yawa, sai ya haifar da ciwon hanta. Wanda idan ba a manta ba na ambaci matsanancin ciwon kai a baya, wanda samuwar hakan yana da abokantaka da ciwon hanta ne.
Hakazalika, amfani da kayan da’a na haifar da raguwar nauyin jikin mutum, canja kalar idanuwa da kuma fitsari zuwa kalar ruwan dorawa.
KAMMALAWA.
A karshe dai ina so na ja hankalin mata masu amfani da kayan da’a da su hankaltu da irin illolin da amfani da su ke janyowa. Kuma ina fata, wadanda ba sa amfani da wadannan magunguna za su fa’idantu da ragaitar da akan fada sakamakon amfani da su. Har ila yau ina so na yi kira ga iyaye mata da su sani cewa shirin nan da su ke yi wa ‘ya’yansu ta hanyar amfani da kayan da’a, yana da matukar hadari ga rayuwar ‘ya’yansu, maimakon su zama mowar mata ko ‘yan lelen mazajensu, kamar yadda suke buri, sai labari ya sauya, wato su koma borar mata.
A fannin mazaje ina so su fahimci kowane dan Adam da yadda Allah Ya halicci shi a dangane da sha’awa da kuma yanayin juriya yayin gudanar da kwanciyar aure, don haka goranta wa mata, zai sa su aikata abubuwan da karshe zai haifar da da-na-sani ne. Sannan ga mazajen da matansu suka kamu da cututtuka sakamakon amfani da kayan da’a, kada su guje su, su gane a dalilin faranta musu da neman burge su matan nasu suka samu kansu a wannan halin. Don haka su rungume su, ta hanyar tashi tsaye har sai an shawo kan matsalar.
Ba zan yi dai kasa a gwiwa wajen kira ga mata wadanda kishi ke sanya su amfani da kayanda’a ba, da su sassauta kishi, su kuma yi kishi irin na matan manzon Allah (SAW). Haka matan da suke gindaya wani sharadi ga mazajensu kafin su kwanciyar aure su sani hakan ba karamin babban laifi ba ne, da idan har ba su daina ba, to za su kasance cikin halaka. Allah Ya kiyaye mu, Ya kuma ba mu lafiya mai amfani, amin.
Nan gaba zan zo da bayanin irin kayayyakin da suka kamata mata su yi amfani da su wajen samun lema a al’aurarsu da kuma iya gamsar da mazajensu ba tare da illa ba.
Domin karin bayani za a iya tuntubar Bashir Liman ta wannan lamba: 0703692565.