Kayan hadin soyayyar ma’aurata
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan kayan hadi ko sinadaran da ke gina ingantacciyar soyayya tsakanin ma’aurata. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da […]
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan kayan hadi ko sinadaran da ke gina ingantacciyar soyayya tsakanin ma’aurata. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Ana lura da wasu muhimman abubuwa wajen fahimtar launi da ingancin soyayyar da ke tsakanin ma’aurata. Wadannan abubuwa su ne kamar kayan hadin soyayya, ginshiki kuma shika-shikan soyayya. Samunsu a kammalance a cikin soyayyar auratayya shi ke sa wannan soyayya ta zama cikakkiya kuma kammalalliyar soyayya; haka rashin daya ko dukkansu daga cikin dangantakar soyayya shi ke nuna nakasun wannan soyayya. Don haka ga bayani kan wadannan muhimman abubuwa don ma’aurata su fahimce su, su fahimci amfaninsu da yadda za su ingantas u cikin rayuwar aurensu don ya kasance dangantakar soyayyarsu ta zama kammalalliya kuma cikakkiya.
- Shakuwa:
Shakuwa na nufin kyakykyawar sanayya da sabo su kullu tsakanin mutum biyu ko sama da haka mai cike da fahimtar juna da tsananin kulawa da sadaukarwa; mutum biyun da suka shaku sosai za ka tarar koyaushe hankali da tunaninsu a hade suke, kuma suna ajiye da kyakkyawan shauki game da juna cikin zukatansu. Shakuwa wata aba ce mai kyau kuma mai dadi, wacce ba ta baci ko ta lalace in dai har an riga an yi ta; domin in ka ji wani ya ce ‘ai mun shaku sosai da wane,’ to yana nufin sun yi zaman jin dadi, kauna da fahimtar juna.
Shakuwa na da wasu muhimman ginshikai da suke tallafarta, wadanda sai sun tabbata a cikin dangantaka sannan ne za iya kiranta shakuwa, ga jerin abuwawan da ke haifar da sahihiyar shakuwa:
- Tarayya
Kafin shakuwa ta kullu, sai ya kasance ana tare na wani lokaci, kuma lokacin da ake taren nan, ana yawaita aiwatar da abubuwan rayuwar yau da kullum tare, ana yawan sabunta sanayya, ta hanyar yin ingantacciyar hira ta fahimtar juna da bayyanar da sirruka ga juna; ana fatar alheri ga juna, ana yin abubuwan faranta rai ga juna, ana taimako da kyautatawa ga juna. Rashin yin tarayya cikin abubuwan yau da kullum na haifar da karancin shakuwa a tsakanin ma’aurata, sai ka ga ma’aurata sun dade tare har sun hayayyafa, amma ba wata sahihiyar shakuwa a tsakaninsu, saboda sun ware kansu ba su yin abubuwan yau da kullum tare. Kowannensu harkar gabansa kadai yake yi, ba wanda ya san abin da dan uwan aurensa yake ciki, kila sai ibadar aure kadai suke yi tare, ko ita din suna yi ne a bukatance, ko kokarin ba da hakkin juna amma ba wata shakuwa cikinta. Yin abubuwa tare shi ne zai haifar da babban jigon shakuwa a tsakanin ma’aurata.
- Sabunta sanayya
Shi ne yawan yin hira da tattaunawa game da kowane bangare na rayuwar juna, domin ta wannan hanya ce ma’aurata za su san tarihin juna, za su san komai da ya faru a rayuwarsu: kanana da manya; masu muhimmanci da marasa muhimmanci; na farin ciki da na bakin ciki; tsofaffi da sababbi. Domin dan Adam yana kara girma, hankalinsa, tunaninsa da shaukin cikin zuciyarsa na caccanjawa. Da sun canja kuma dole halayyarsa da yanayin cudanyarsa da mutane su canja. In ya kasance ma’aurata ba su sabunta sanayyarsu, wannan zai haifar da rashin fahimtar juna a tsakaninsu, wanda wannan wata babbar baraka ce da ke dakushe kaifin rayuwar aure ko ta kashe ta gaba daya.
iii. Fahimatar juna
Wannan shi ne babban jigo na shakuwa a tsakanin ma’aurata, ya kasance sun fahimci junansu ta kowace fuska, ya kasance hankali, tunani da ra’ayoyinsu sun zamo daya a mafi yawan lokuta; sun san abubuwan so da kyamar junansu, sun fahimci yanayin halayya da shaukin junansu; wannan zai taimaka musu kiyaye duk wani abu da zai kawo gardama ko husuma a tsakaninsu, kuma zai haifar musu da haduwar kai, yarda da aminta da juna.
- ib. Yarda
Wannan shi ne ya kasance ma’aurata sun aminta da juna ta kowace fuska, sun fahimci karfi da raunin juna ta kowace fuska kuma sun aminta da haka, wani abu da ya yi rauni ko ya kasa a cikin halayya ko kasantuwar dayansu bai rage daraja da kimarsa ba a idon dayansu.
- b. Haduwar hankali da tunani
In ma’aurata ya kasance yanayin hankalinsu ya hadu da juna, tunaninsu game da rayuwa ya zama daya, ra’ayinsu daya game da mafi muhimman al’amuran rayuwarsu, sannan bukatunsu da hangen da suke wa rayuwa sun zama daya, to wannan zai sa saukin fahimtar juna a tsakaninsu, kuma zai karfafa shakuwarsu.
Zan dakata a nan, sai mako na gaba inshaAllahu za mu ji bayani kan sauran kayan hadin soyayya. Da fatar Allah Ya sa mu kasance a cikin kulawarSa a ko yaushe, amin.