Kayan hadin soyayyar ma’aurata (3)
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan kayan hadin soyayyar ma’aurata. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin. […]
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili da fatar Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan kayan hadin soyayyar ma’aurata. Da fatar Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
3. Abota: Abu na uku cikin kayan hadin soyayyar ma’aurata shi ne ya kasance akwai kyakykyawar abota a tsakanin ma’aurata. Abota wata kyakykyawar zumunta ce da ke kulluwa a tsakanin mutum biyu ko sama da haka wacce ke dauke da kyakykyawar sanayya da fahimtar juna; yarda da amincewa, so da kauna da kuma mutunta juna.
Kyakykyawar abota na samuwa ce lokacin da mutum biyu ma’abota kauna da amintar juna, suka kasance suna yawan haduwa a kai-a kai, kuma in sun hadu suna sabunta sanayya ta hanyar tattaunawa game da kowane bangare na rayuwarsu da rayuwar mutane mafi kusanci da su da hirar abubuwan da suka sa a gaba a wannan lokaci da tattauna abubuwan da suka sha musu kai ko wasu matsaloli da suke fama da su, taimakon juna ta kowane bangare, ba juna shawara da karfafa gwiwa da bayyanar da sirrukan zuciyarsu ga junansu; da yin abubuwan yau da kullum tare kamar cin abinci, wasanni, ziyara, sada zumunci da hirar raha da sauransu.
A takaice dai abota wata dangantaka ce mai kyau mai dadi kuma mai cike da alherai mara iyaka. Cikakkiyar abota ita ce wacce aka kulla saboda Allah kadai ba don wata bukatuwa ta duniya ba; sannan halayen abokan ya zo daya, hakan sai ya haifar da kyakykyawar fahimtar juna da shakuwa a tsakaninsu.
Abota mai rauni kuma ita ce wacce aka kulla a kan wata bukata ta duniya kamar kudi, matsayi, daukaka ko don son burgewa.
Abota cikin rayuwar aure
Abota tana da matukar muhimmanci cikin rayuwar aure, domin abota ita ke haifar da shakuwa a tsakanin ma’aurata, don haka in ma’aurata ba su zama abokan juna ba, zai yi wuya a samu shakuwa da sabo mai kyau a tsakaninsu.
Fuskokin abotar ma’aurata
Shakikan Juna: Su ne ma’auratan da suke da kammalalliya kuma cikakkiyar abota, sun fahimci kowane bangare na rayuwar junansu, tun daga shauki, halaye abubuwan so da ki, karfi da raunin juna da sauransu. Sannan ba su shayin gaya wa junansu dukkan sirrukansu, ba su da abokin shawara da ya wuce su yi da juna. Suna tsananin bege da kaunar juna; ba abin da suke rabawa a cikin rayuwar aurensu, komai na kowa ne ba mai hana daya wani abu daga cikinsu, damuwar daya damuwarsu ce su duka, ba su ware juna a cikin komai na harkokin rayuwarsu. Akwai tsananin mutunta juna a tsakaninsu ta yadda ko sun samu sabani, bai sa su daina mutunta juna kuma nan da nan suke warware sabanin da ke tsakaninsu.
Aminan Juna: Ana samun irin wannan abotar tsakannin ma’aurata, ya kasance sun yarda da juna, sun amince wa juna, ba cin amana ba munafunci a tsakaninsu, sannan ba su zaluntar juna, amma duk da haka sun sanya wasu iyakoki a cikin dangantakarsu da ba su ketarewa: misali, ba kowane irin sirri ba ne suke iya sanar wa junansu, kamar a ce miji bai san arzikin jakar matarsa ba, ita ma ba ta san zurfin aljhunsa ba; ko ya kasance abubuwan da maigida ya san ba su shafi uwargidansa ba bai sanar mata ita ma haka; ko ya kasance abokansu ko kawaye su ne abokan shawara ba ga junansu ba.
Masu Fuska Biyu: Su ne wadanda a fili kamar shakikan juna suke, ta yadda ba su iyakance muhimman abubuwa daga junansu ba, suna shawartar juna, suna tattauna abubuwan da ke cikin rayuwarsu ga junansu, amma a zuci ba su aminta da juna ba, a zuci suna jin haushin juna, a zuci suna zaluntar juna; misali: duk matar da ke fadan laifuffukan mijinta ga ’yan uwa ko kawayenta, ko mai yin asiri don mallake mijinta, ko namijin da ke bin mata a waje da sauransu, to komai kyan dangantakarsu a zahirance, tana da babban gibi domin saboda wannan mummunan sirri da suke boyewa wanda in zai bayyana gaba daya zai share soyayyar da ke tsakaninsu.
Abokan Hamayyar Juna: Akwai ma’auratan da abota ta asali ’yar kadan ce cikin dangantakarsu don haka koyaushe ba fahimtar juna, ba aminci a tsakaninsu, sun zama kamar abokan hamayya, abin da bai kai ya kawo ba sai ya haifar da gardandami da jayayya a tsakaninsu.
Karin bayani
A mafi yawan auratayyar wannan zamani, an fi samun dangatakar abota ta biyu da ta uku; wato aminan juna da masu fuska biyu. Shakikan juna da abokan hamayya kuwa su suka fi karanci. Da so samu ne, ya fi dacewa da alfanu a ce dukkan ma’aurata su kasance shakikan abokai, don cimma wannan inganci cikin rayuwar aurensu, sai ma’aurata su yi kyakykyawan bincike tare da yin dogon nazari don gano ina ne dangantakar abotarsu take da gibi, sannan su dage da dukkan kokarinsu wajen ganin sun cike wannan gibi don karuwar farin ciki da kwanciyar hankali cikin rayuwar aurensu.
Sai mako na gaba inshaAllah da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.