Kayan kwalliyar da ke illata ido
Ya kamata a san cewa yawaita caba ado da mascara da dangoginsa a ido yana illata shi.
Yana da kyau a dinga tsallake wasu kwanaki wajen kwalliyar ido irin ta zamani. Kada ya kasance a kullum sai an yi.
Bincike ya nuna cewa yawaita caba ado da mascara da makamancinsu a ido yana illata shi.
Don haka ne a yau na kawo muku ababen kwalliya da suka kamata a yi la’akari da su domin kada su illatar da ku.
• Eye Liner: Mace ta samu kwalli ko kajol dinta yafi mata sauki.
Domin yana dauke da sinadarin da idan ya taba hawaye yana saurin zuwa kwakwalwa wanda idan aka ci gaba da sawa zai iya rage ganin mutum.
• A kula da kayan kwalliyar da lokacinsa ya kare.
Wasu matan suna amfani da kayan kwalliya fiye da shekara biyu ba tare da sun duba ko lokutan amfani da su sun kare ba.
Amfani da irin wadannan yana da hadari ga ido.
• Amfani da gashin idon kanti: yawan amfani da gashin ido yana da babban hadari ga ido domin da gam ake sa shi.
Bayan an cire, yakan janyo kumburin ido da fesowar kuraje.
• Amfani da ‘contact lense’: Wannan kuma a kwayar ido ake sakawa.
Tana kama da leda, wanda yake dauke da launuka da dama kamar su shudi da ja da sauransu.
Mata kan dora shi a kan kwayar idonsu domin canza launinsa.
Yawan amfani da wannan abu yana jawo makanta.
• Da zarar anga ido yana yawan hawaye ko yawan kaikayi a yi maza aje asibiti.
A daina bari sai ciwo ya yi tsanani kafin a ga likita.