Kayan kwalliyar da ta dace da fata

Ya kamata mata su san irin kayan kwalliyar da ta dace da fatarsu saboda amfani da kayan kwalliya ko man shafawa wanda bai dace da fatar ba na kawo illa ga fatar. A yau na kawo mana shawarwari game da masu gaustin fata ko fata mai maiko da kuma mara gausti. Za a iya samun […]

Kayan kwalliyar da ta dace da fata

Ya kamata mata su san irin kayan kwalliyar da ta dace da fatarsu saboda amfani da kayan kwalliya ko man shafawa wanda bai dace da fatar ba na kawo illa ga fatar. A yau na kawo mana shawarwari game da masu gaustin fata ko fata mai maiko da kuma mara gausti. Za a iya samun wadannan nau’ukan man a shagunan da ake sayar da kayan kwalliyar zamani.

Fata mai gautsi:  

•A nema ‘double-duty’ fandesho idan za a sanya fandesho, domin maikon da ke cikin fandesho na taimakawa gautsin fata sosai.

• Kada a rika sayan man da aka yi su da kayan maye domin hakan na bata fata.

• Ya kamata a rika yawaita shafa man jiki akai-akai.

Fata mai maiko: hakan na faruwane saboda yawan kiba ko gumi da ke jiki.

• A sami ‘cleanser’ wanda ke tafiyar da datti da maikon fuska wanda kuma zai iya kashe ‘ya’yan cuta da ke haifar da kurarragen fuska.

• Kada a rika amfani da man da zai canza kalar fata a kan fata mai maiko domin yin hakan na dada maikon fuska.

• A sayi fandesho da hoda wanda zai tsayar da maikon fuska.

• A rage yawan shafa fuska da rana saboda tafin hannunmu na dauke da na ta maikon, idan anyi hakan, kara maiko yake yi a fuska.

• Kuma na yawaita canza gidan filo don tsabta.

Fata mara maiko da mara gautsi: irin wannan fatar bata da gautsi da kuma maiko. Za a ganta babu kurarraji, kuma irin wannan fatar na canzawa saboda yanayin wuri;ko damina ko rani ko kuma hunturu.

• Ana sayan fandesho da ake rubuta ‘normal skin’ a kanshi kamar man ‘TRUblend’da sauransu.

• Za a iya shafa nau’ukan da zasu sa maiko a kan irin wannan fata da hunturu.

• Kuma a zama ana tare da hoda kowani lokaci saboda idan zafi yazo za a iya shafawa domin fatar na canzawa ne saboda yanayi.