Kayan Najeriya ba su da daraja a Turai – ‘Yan kasuwa
Gwamnatin Tarayya na yin wani sabon yunkuri na kyautata safarar kayan gona zuwa kasashen waje da nufin fadada kafofin samun kudin-shiga maimakon dogaro da man fetur. To amma sai dai kuma wasu ‘yan kasuwa sun ce duk wani kokari da za su yi don tallata kayan Najeriyar zuwa kasashe ketare, da wuya ya yi tasiri. […]
Gwamnatin Tarayya na yin wani sabon yunkuri na kyautata safarar kayan gona zuwa kasashen waje da nufin fadada kafofin samun kudin-shiga maimakon dogaro da man fetur. To amma sai dai kuma wasu ‘yan kasuwa sun ce duk wani kokari da za su yi don tallata kayan Najeriyar zuwa kasashe ketare, da wuya ya yi tasiri.
‘Yan kasuwar dai sun bayyana cewa suna cin karo da matsaloli a wannan harka, ciki kuwa har da karancin jari da rashin darajar kayan Najeriyar a kasuwannin kasashen Turai.
A cikin wata hira da gidan rediyon BBC ya yi da wani kwararren dan kasuwa a kungiyar ‘yan kasuwar Jihar Kano, Alhaji Kamal Abdulkadir Mustapha, wanda kuma ke fataucin kaya zuwa kasashen Turai, ya bayyana cewa, kayansu na fuskantar kalubale sosai a kasashen waje.
Yana mai cewa saboda yawanci ‘yan Najeriya sun yi suna wajen aika abubuwa wanda suke na jabu, marasa nagarta, hakan ya sa idan ka kai kaya daga Najeriya ake fuskantar kalubale.
“Wannan dalili ne ya sa wasu ‘yan kasuwar Najeriyar kan gwammace su kai kayansu Nijar ko Ghana ko kuma Cotonou, domin su auna kayansu su tura su ta can, don su samu biyan bukata wato ta yadda idan an kai su kasashen waje za a saye su daraja”.
A kan wadannan dalilai, ‘yan kasuwar suka ce dole ne sai gwamnati ta taimaka wajen kare martabar kayayyakin da suke samarwa a idon kasashen duniya, idan ana so kasuwancinsu ya bunkasa.
To yanzu dai, gwamnatin Najeriyar ta ce bisa la’akari da irin kalubalen da ‘yan kasuwar ke fuskanta, hakan ya sa hukumar bunkasa fataucin kayan Najeriya zuwa kasashen waje ta fito da wani shiri na kara wa ‘yan kasuwar kwarin gwiwa.
Hukumar dai ta na hada wasu fatake a wasu manyan birane domin wayar musu da kai a kan sabon shirinta game da bunkasa fitar da kayayyakin amfani gona zuwa kasashen waje.